Connect with us

TATTAUNAWA

Duk Da Taron Dangi Sai Da Kwankwaso Ya Kai Keyar Gwamnatin Ganduje Kasa – Hon. Garo

Published

on

Rt. HON. NASIRU SULE GARO Shi ne Wakilin Al’ummar Gwarzo da Kabo a Majisar Wakilai ta tarayya, Guda cikin Shuhada’un Kwankwaso, matashi na gwagwamarya mai tabbatacciyar akidar da baya rawa duk da irn matsin lambar da ya fuskanta daga siyasar cikin gida. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA Jim Kadan da Kammala raba tallafin kayan sarrafa audugar Mata da ya shiryawa mata sama da 100 ‘yan asalin Kananan Hukummi biyu da yake wakilta, Nasiru Sule Garo ya gudu har da zamiya inda ya bayyana cewa duk da taron dangi da aka yiwa Kwankwaso a Kano karshe said da yabkai su kasa warwasa. Haka Kuma ya tunawa masu adawa da kyakkyawar niyyar Kwankwaso cewar sun makara . Ga dai yadda tattaunawar ta kasnace:Farko za mu so mu ji wanda muke tare da shi?
Alhamdulillahi da sunan Ubangijin da barci ko gyan-gyadi baya riskarsa, sannan kuma muna kara salati ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW, kamar yadda aka sani ni sunana Nasiru Sule Garo wakilin al’ummar Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilai ta tarayya, haifaffen garin Garo dake cikin karamra Kabo a Jihar Kano, na yi karatun Alkur’ani kamar yadda yake cikin tsarin addininmu na musulunci sannan kuma na samu yin ilimin zamani mai zurfi. Sai kuma harkokin kasuwanci sannan kuma muka tusnduma cikin harkokin siyasa wanda har Allah cikin jinkansa da amincewar al’ummar da mu ke tare dasu suka aminta da nagarta ta suka tura ni na wakilce su a majalisar wakilai ta tarayya. Ina da aure da kuma ‘ya’ya, Alhamdulillahi.
Honarabul kasancewar makonnin da suka gabata an gudanar da zabukan shugaban kasa da na wakilan majalisar Dattajai da na wakilai, kuma an ji yadda sakamakon zaben ya biyo baya a mazabar da ka ke wakilta ta Gwauro da Kabo, ko me zaka ce kan wannan sakamako?
Alhamdulillahi kamar kullum kuma kamar yadda aka sani ni ban shiga siyasa ko a mutu ko ayi rai ba, musamman ganin irin kaunar da al’ummar da nake wakilta ke yi min, wannan tasa sakamakon zaben da ya bayyana muka kalle shi tare da kyautatawa Allah zato, kuma daman cewa na yi Allah duk abin da yafi alhairi ya zaba mana. Muna kuma kyautata zato wannan bakaramin alhairi Allah ke nufi da matsayin sakamakon zabe ba.
Amma ranka ya dade mun kalli halin da al’ummar wannan yanki suka shiga jin ba kaine ka lashe zaben ba, hankalin kowa ya tashi, amma kai ga abin da ka ke cewa, mene sirrin hakan?
Kamar yadda ka sani ita siyasa hali ce kowa da irin nasa, ni abin da na yarda shi ne na samu kyakkyawar shaidar al’ummar da nake wakilta, kuma alhamdulillahi kamar yadda ko ku ‘yan Jaridu kun shaida kuma kun je yankin namu kun ji abin da jama’a ke cewa, wannan wani al’amari ne ba wayona bane hikimace ta Allah madaukakin sarki. Wanda da shi muka dogara kuma shi muke fatan ya yi mana jagora aikin dukkan al’umuran muna yau da kullum.
Kamar yadda kowa ya gani mun yi kokarin yiw aal’ummar kyakkyawan wakilci mai cike adaci da kuma kaunar cigaban jama’armu, wannan tasa kullum muke da kyakkyawar alaka da jama’a da suka tura ni wakilcin su. Don haka kullum idan sun yunkura zasu nuna damuwarsu na kan fada masu ubangijin d aya baku ni har kuke mini wannan kyakkyawa zato yana nan tare damu ba zai wofantar damu da yardar Allah kuma suna fahimtar haka a ko da yaushe.
Kai ne wakilin da a ka yi ittifakin ba ka gudun jama’ar ka kamar yadda suma basa gudunka, shin ko menene sirrin hakan?
(Dariya) ‘Yan Jarida kenan, ni a tunani na ban ga dalilin da zai sa jama’a su bata lokacinsu wajen tsayawa su zabi mutun ba, kuma ace wai idan ya samu nasara ya far ashigarwa al’ummarsa layar zana, wannan ba dabara bace a wurina.kalamar daya ce, kuma ita na aminta da ita, idan jama’a ta suka zo da bukata matukar ina da hali babu jeka ka dawo, idan kuma bani da halin cika bukatun da aka zomin dasu, zan yi masu kyakkyawan lafazi da kuma cikakken bayani wanda zai gamsar dasu, ba tare da na yaudare suba, yaudara itace abin da nafi tsana a rayuwata, don haka ina yin duk mai yiwuwa domin fahimtar al’ummata hakan tasa suma suka fahimci ne gwargwadon iko.
An gudanar da zaben Gwamna a Jihar Kano, kuma Jam’iyyar ku ta PDP Kwankwasiyya ce ta samu nasara amatakin farko duk an ce zaben bai kammala ba, shin ko me zaka ce kan wannan kwarya-kwaryar nasara da kuka samu?
Alhamdulillahi, wannan Nasara daga Allah ne domin shi Allah baya tozarta ladan masu yidomin sa, Jagoranmu akwai abubuwan da lokaci ba zai bada damar bayyana su baki daya ba wanda ya yiwa al’ummar jihar Kano, kuma mun tabbata anyi duk mai yiwuwa domin rusa wadancan kyawawan ayyuka domin shafe sunansa a tarihin Jihar Kano, amma sai suka manta Allah ke rubuta sunan basu ba. Ko hasidin iza hasada ya aminta da irin tagomashin da bangaren ilimi ya samu, inganta hanyoyi, kawata birnin Kano, samar da gadojin kasa da na sama a jihar Kano wanda babu irinsu a fadin Nijeriya ba ma Jihar Kano ba.
Haka kuma shi ne Gwamna daya tilo a Nijeriya da ya gina Jami’o’i biyu Jami’ar kimiya da fasaha dake Wudii da kuma North West, sai makarantu 24 da suka shafi harkokin inganta al’umma kai tsaye, ga kuma shirin nan na CRC wanda ake ciyar da daliban makarantun firamare tare da basu Uniform kyauta, sai kuma tura ‘ya asalin Jihar Kano zuwa Kasashen waje
domin karin ilmi tare da samun digiri har da digirgir a Jami’o’in cikin gida da waje. Inganta hanyoyin samunkarin kudeden shiga wanda basu shafi mai karamin karfi ba. Saboda haka ire iren wadannan abubuwan alhairi ganin Sanata Kwankwaso ya shelanta cewa wadannan abubuwa idan gwamnatin da ta karbe shi ta yi kokarin rusa su, yace babu shakka zai nade kafar wando ya dawo, kuma hakan ce ta faru. Ganin idan ya yi Magana tana tabbata hakan ta sa a ka yi masa taron dangin son zuciya da niyyar sai an kai shi kasa. Amma ta Allah ba tasu ba dukkan su ya hade su wurin guda ya make su tare da lashe zaben kujerar Gwamna da ‘yan majalisar dokoki masu yawa a zaben da ya gudana ranar asabar 9 ga watan March, 2019.
Kwanaki kadan kafin gudanar da zaben gwamna an hange ka kana kaddamar da wani shirin horar da matan karkara yadda ake samar audugar mata, shin mene dalilin shirya wannan taro?
Alhamdulillahi kamar yadda na ambata tun da farko mu Kwankwasawa tarbiyar da muka samu itace cika alkawari, wannan tasa alokacin da na ke yawon yakin neman zabe a kananan Hukumomin da nake wakilta na duba matsalar da mata ke fuskanta wajen yawan mutuwar mata a lokacin nakuda da kuma kananan yara ‘yan kasa da shekara biyar, hakan tasa na kuduri aniyar samar da wani tsari da zai taimakawa matan mu na karkara wajen samun saukin tanadin auduga alokacin jinin al’ada. Saboda haka na nemi hadin guiwa da ma’aikata sufurin jiragen ruwa tare da gogaggun masana matsalolin mata, kuma na samu kyakkyawar shawarar abin da ya kamata a yi wanda zai amfani mata musamman na karkara, domin kudin sayen audugar bature ya fi karfin mutanen mu na karkara.
Wannan tasa muka zakulo mata 100 daga kananan Hukumomin Gwarzo da Kabo wadanda aka koyawa yadda zasu samar da audu mai tsafta kuma wadda wanke ta za a dinga yi bayan an gama al’ada, sai a aje sai kuma wani watan. An koyar da yadda za a saka audugar, an bayar da sinadaran wanke audugar aduk lokacin da a ka yi amfani da ita, kuma zata jima ana
amfani da ita, wanda hakan ya samar da tsumi da tanadi da ‘yan kudi kadan. Kuma Alhamduillahi mata sun koyi wannan aiki yanzu haka bayan sun koma gidajensu suma sun shiga aikin koyar da sauran matan a inda suke.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!