Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Karfafa Kasuwar Hannun Jari A Nijeriya

Published

on

Ministar kudi uwargida Zainab Ahmed ta sanar da cewar, Gwamnatun Tarayya ta shirya karfafa kasuwar hannun jari ta kasa ta hanyar adana kudi.
Ta sanar da hakan ne a jawabin ta a Abuja a ganawar data yi da wakilan Cibiyar CMMPI inda ta ce, gwamnatin tana son kafa kwamitin ajiyar kudi na kasa na NSC da zai gabatarwa da gwamnatin shawarwarin sa akan hanyoyin da suka dace na adana kudi da zai taimaka wajen ciyar da tattalin arzin kasar nan gaba.
Ta yi nuni da cewar, akwai bukatar yan kasar nan ta rungumi dabarun adana kudi yadda suma zasu shiga kasuwar don adama dasu da kuma kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
Acewar ta, akwai bukatar a habaka zuba jari na cikin gida ba wai kawai mutane su dinga zuwa ko ina don neman riba ba.
Ta bayykna cewar da gaske ne a yanzu amfi mayar da hankali a fannin banki kuma akwai bukatar a magance wannan matsalar, wadda za’a iya magance su a cikin gaggawa za’a yi wanda kuma ba zai yuwu ba za’a sanya shi ana dogon zango.
Ta bayyana cewar, gwamnatin ta damu da kasuwar kuma za ta yi aiki da CAMMIC don tabbatar da samar da daidaito a kasuwar, ta kara da cewar, gwamnati tana sane da mahimmancin da masu zuba jari na kasar waje suke dashi a kasuwar, musamman don kara masu zuba jari na cikn gida a kasuwar kwarin gwaiwa.
Ta bayyana cewar gwamnatin tana yin kokari wajen mayar da hanakli a wasu fannonin na tattalin arzkin kasa yadda zata kaucewa dogaro da man fetur da iskar gas.
Ta bayyana cewar shugaban kasa yana kara mayar da hanakali a fannin aikin noma
A nashi jawabin shugaban CAMMIC Mista Olutola Mobolurin ya yi nuni da cewar akawi bukatar gwamnatin ta mayar da hankali akan kasuwar ta hannun jari ganin cewar tana daya daga cikin ginshikan tattalin arzikin kasa.
Shugaban ya ce kasuwar tana da ka’idoji kuma tana taimakawa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan.
Shugaba Mobolurin ya yi kira da a kafa kwamitin, musammandon kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
A karshe ya zayyana wksu daga cikin nasarorin da Cibiyar tasa ta samu da suka hadada, wayar da kai akan hada-hadar kudi, dabarun adana kudi, samar da damar zuba jari, ya kara da cewar, a 2019 CAMMIC zata fara sabunta tasawira don kara bayar da goyon baya wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan.
Daraktar Janar ta Riko ta Kasuwar ta SEC Mary Uduk ta ce hukumar tana yin aiki kafada da kafada da kasuwar don kara habaka kasuwar da kuma bata kariya daga durkushewa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!