Connect with us

LABARAI

Kano: Ni Zan Lashe Zaben Da Za A Sake Fafatawa –Abba K. Yusuf

Published

on

Dan takarar geamna na jam’iyyar PDP a jihar kano, Abba Yusuf, ya bauyana cewa, lallai shi ne zai ssake lashe zaben da za a sake gudanar a wasu sasssan jihar kwanan nan.
A ranar Talata ne, INEC ta bayyana rashin kammaluwar zaben da aka gudanar na gwamnan jihar Kano a wani zazzafan fafatawa da aka yi a tsakanin gwamnan mai ci Abdullahi Ganduje da Kabir Yusuf.
Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaba kwamitin tatara alkalummar zaben na jihar Kano, Bello Shehu, y ace ya zama dole sake fafatawa ne saboda jimillar kurui’un da aka soke ya zarce banbanci dake a tsakanin yan takarar na jam’iyyar PDP da kuma jami’iyyar APC.
Yacikin dalilan da suka haddasa soke a tare da sake zaben a wasu wurare a ciki kananan hukumomi 22 dake a fadin jihar,sun hada da aringizon kuri’u da kuma tasjin hankali a wurare da dama. Ya kuma bayyana cewa, mazabu 172 a fadin jihar wannnan sokewar ya shafa.
Amma a sanarwa day a bayar jiya Talata, Kabir Yusuf, ta hannun jami’in watsa labaransa, Sanusi Dawakin-Tofa, y ace jam’iyyar APC c eta tafka magudin da haifar da soke sakamakon da suka fito daga wasu mazabu har 172.
“Jama’ar Kano na ganin yadda makiya tsarin dimokradiyya cikin manyan gwamnatin s=da suka hada da mataimakijn gwamna Nasiru Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Garo da shugaban karamar hukumar Nassarawa Lamin Sani Kawaji suka lalata kayan zabe da nufin kawo cikas ga kokarin nadara da ake ganin jam’iyyar PDP ta kamo hanyar samu,” inji shi.
Dan takarar gweamnan ya kuma bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta samu bayanan dake nun a cewa, gwamnati ta buka takardar dzabe fiye da katan 500 a ‘Kano State Printing Press’ a ka kuma rarrraba zuwa runfunar abe, yan sanda sun kuma samu nasar kama katan 10 na kuri’un da aka buga.
“Muna fatan za a hkunta dukkan wadanda aka samu da laifin zabe dion haka ya zama darasi ga makiya tsarin dimokradiyya.
“Muna kumna kira ga duykkan magoya bayanmu das u kasance a natse don kuwa muna da tabbacin samuh nasara a zaben da za a sake gudanar wa.
“ya kamata magoya bauynmu su kwana da saniun cewa jam’iyyar PDP c eke a kan gaba kuma za a gudanar da zabe ne a yankin da muke da dimbim magoya baya,” inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!