Connect with us

LABARAI

Muna Neman Soke Zaben Kujerar Gwamna A Adamawa -APC

Published

on

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Adamawa, ta bukaci hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta soke zaben kujerar gwamna da ta gudanar ranar Asabar da ta gabata a jihar.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Yola, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas Kwamared Salihu Mustafa, ya ce basu amince da sakamakon zaben a kananan hukumomin jihar shida ba, domin ba’ayi zabe da na’uran tantance jama’a a kananan hukumomin ba.
Kwamred Salihu Mustafa, wanda shine jami’i mai tattara sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da na gwamna a jihar, ya kuma yi zargin zaben da dama hukumar zabe ta ce bai kammala ba cike yake da rashin inganci.
Ya ce “muna son mu bayyanawa duniya irin tsantsan rashin ingancin da yake cike da zaben kujerar gwamna da hukumar zabe INEC ta yi a Adamawa, mu a jam’iyyar APC bamu amince dashi gaba daya ba.
“mu muna da ingantattun shaidun da ke nuni da cibiyoyin zabe da dama ba’abi ka’idar doka ba, wasu gurare ba’ayi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a ba, wasu kuma kuri’u sunfi yawan mutanen da sukayi rigista.
“kuma masu sa mana ido (agents) an koresu, kamar karamar hukumar Hong an kashe mana mai sa ido guda, saboda haka muka kai kokenmu ga hukumar zabe a matakin jiha, amma akaki amsa” inji Salihu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin arewa maso gabas Salihu Mustafa, ya bayyana kananan hukumomin da jam’iyyar ke neman hukumar zabe INEC ta soke zabensu da Demsa, Lamurde, Numan, Guyuk, Michika, Madagali da kuma Hong.
A ranar Litinin ne dai hukumar zabe ta kasa INEC ta sanarda zaben da ta gudanar a jihar ranar Asabar da cewa bai kammala ba, saboda kuri’un da’aka soke a zaben ya’yi yawa.
To sai dai wannan na zuwa lokacin da jam’iyyar PDP ke ikirarin hukumar zabe INEC ta sanarda dan takararta a zaben Ahmadu Umaru Fintiri, a matsayin wanda ya lashe zaben, domin kuwa a ganin ko an sake zaben ba zata canja zani ba.
Da yake jagorantar wani taron manema labarai a Yola fadar jihar tsohon gwamna kuma jigon jam’iyyar Boni Haruna, ya c su sun amince da sakamakon zaben cewa su suka lashe zaben bisa la’akari da yawan kuri’un dake tsakanin jam’iyyar PDP da APC.
Ya ce rashin ayyana jam’iyyar PDP da cewa ita ta lashe zaben ba’abin amincewa bane, ba su amince da haka ba, ya ce domin yawan adadin mutanuda hukumar zaben INEC ta yiwa rigista ba duka zasu kada kuri’a ba, don haka babu bukatar sake wani zabe.
Ya ce “munyi bincike yawan adadin mutanen da sukayi rigista ya’yi kasa da adadin kuri’un da mukaci zabe, to akanme kuma za’ace za’ayi wani zabe? INEC ta ayyana dan takararmu a matsayin wanda ya lashe zabe Kasai” inji Boni Haruna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!