Connect with us

KASUWANCI

NECA Ta Yaba Wa CBN Kan Cire Tallafin Shigo Da Yadudduka

Published

on

Kungiyar NECA ta kasa ta jinjinawa Babban Bankin Nijeriya CBN akan cire tallafin shigo da yadudduka zuwa cikin Nijeriya.
Darakta Janar na kungiyar ta NECA Mista Timothy Olawale ne ya yi yabon a cikin sanarwar da ya fitar a jihar Lagos a ranar Juma’ar data gabata.
Mista Timothy Olawale ya bayyana cewar, matakin da Babban Bankin na CBN ya dauka akan hakan, zai taimakawa fannin masakun dake kasar nan, inda ya ce, ana kashe samada dala biliyan 4 wajen shigo da kayan masaku cikin kasar nan.
Darakta Janar ya shawarci gwamnatin tarayya data gaggauta dikile ayyukan masu yin fasakaurin ganin cewar, suna yiwa kokarin da gwamnatin tarayya take yi na farfado da masakun dake kasar nan da suka durkushe.
Acewar Darakta Janar, Babban Bankin Nijeriya ya taimaka matuka wajen sa ya takunkumin.
Samada Dala biliyan 4 da ake kashewa na shigo da kayan masakun, za’a iya yin amfani dasu wajen ciyar da wasu fannonin a kasar nan.
Da yake yin nuni akan alfanun da masakun suke dasu a kasar nan a shekarun da suka gabata
Olawale sun samar da ayyukan yi ga ma’aikata kashi 25 bisa dari a kasar nan, musamman ga masakar farko da aka kafa a shekarar 1956.
Ya bayyana cewar, masaku na zamani a Nijeriya sune, ta Kaduna da aka kafa a shekarar 1956 sai kuma ta Arewa da aka kafata a shekarar 1987, inda a lokacin akwai masaku guda 37 a cikin kasar nan da keda kimanin na’urorin aiki guda 716,000 da kuma sauran kayan aiki guda 17,541.
A duk shekara, ana samun karuwar data kai kashi 65 daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1991, inda kuma aka dauki ma’aikata kimanin kashi 25 bisa dari a masakun wadanda a lokacin ake tunkaho dasu a Nijeriya.
Ya yi nuni da cewar, akwai bukatar gwamnatin ta kara sanya ido akan iyakokin kasar nan don dakile ayyukan masu fasakauri don baiwa masakun kasar nan kwarin gwaiwa.
Ya kara da cewar, kara zagewar da Kwastam da hukumar kula da shige da fice da sauran hukumomi suke yi zai taimaka matuka wajen tabbatar da tsaro a iyakokin kasar nan.
Olawale a karshe ya shawarci gwamnatin tarayya akan kada ta gajiya akan kokarin da take yi na samar da kyakyawan yanayi ga masakun kasar nan
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!