Connect with us

LABARAI

PDP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Borno

Published

on

Jam’iyyar PDP a jihar Borno, ta sa kafa ta yi fatali da sakamakon gwamnan jihar, wanda hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta shelanta a jihar- wanda a ciki ta bayyana Farfesa Zulum, na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben kujerar ta gwamna.
Baturen tattara sakamakin zaben da hukumar INEC ta tura a jihar, Alhassan Gani, ya ayyana cewa Farfesa Zulum wanda ya samu kuri’u 1, 175, 440 shi ne ya samu nasarar lashe zaben, bayn ya doke abokin takarar sa, Muhammad Imam, na jam’iyyar PDP, mai kuri’u 66, 117.
Babban jami’in hukumar INEC, Gani ya kara da cewa, zaben wanda aka gudanar a jihar, wanda yan takara daga jam’iyyu 32 suka yi zawarcin sa a jihar.
Sa’ilin da yake bayyana matsayar su dangane da sakamakon zaben, sakataren tsare-tsaren jam’iyyar PDP a jihar Borno, Umar Bello, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta sa kafa tare da yin fatali da wannan sakamakon da INEC ta sanar, tare da bayyana rashin sahihancin sa.
Har wa yau kuma, Malam Bellon, wanda kuma shi ne wakilin jam’iyyar PDP, a cibiyar tattara sakamakon zaben, inda ya kekasa kasa tare da kin amincewa ya rattaba hannun sa a takardar sakamakon hukumar INEC din, sannan ya shaidar da cewa, ba da jimawa ba jam’iyyar PDP za ta bayyana matsaya dangane da sakamakon.
Yayin da a nashi bangaren kuma, shuganan jam’iyyar APP, Abdulkadir Grema, bayyana farin ciki ya yi dangane da yadda zaben ya gudana a cikin tsanaki, a jihar Borno.
A hannu guda kuma, da yake bayyana matsayar, shugaban jam’iyyar ASD a jihar, Alhaji Abba Aji, kira ya yi ga sauran yan takarar da suka fadi da cewa su rungumi kaddara tare da mara wa sabuwar gwamnati mai zuwa a jihar baya.
Haka zalika kuma, ya jinjina wa kokarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar dangane da hubbasar gudanar da zabukan cikin tsanaki, gaskiya da adalci ga kowa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!