Connect with us

LABARAI

Satar Akwati: Abin Da Ya Sa Ba Mu Harbe Mataimakin Gwamnan Kano Ba –’Yan Sanda

Published

on

’Yan sanda a Kano, sun yi bayani a kan dalilin da ya sanya ba su harbi mataimakin gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo ba, a wajen tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Nasarawa, a ranar Lahadi.
Gawuna da Garo, sun je cibiyar tattara sakamakon zaben ne a ranar ta Lahadi, tare da wasu ‘yan banga wadanda ake zargin Kwamishinan ne ya jagorance su, inda suka yayyaga takardun sakamakon zaben inda hakan ya haifar da tashin hankali.
Da yake magana da manema labarai, Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Haruna Abdullahi, cewa ya yi, “An ba mu horo ne kan kare mutane da dukiyoyin ‘yan Nijeriya. An horar da mu ne domin mu yi kamu ko mu gayyaci duk wanda ya sabawa dokar kasa, mu maido da shi a kan hanya. Amma ba a horar da mu don mu kashe kowa ba.
“Aikin mu shi ne tabbatar da ana bin doka a Jihar Kano, mu tabbatar mutane suna girmama doka, amma ba mu yi kisa ba. duk wadanda suka sabawa doka a wannan cibiyar tattara sakamakon zaben mun kama su,” in ji shi.
Ya ce, Garo da Alhaji Lamin Sani, shugaban karamar hukumar ta Nasarawa, an kama su a bisa zargin sun lalata takardun sakamakon zabe.
Ya ce, amma Gawuna, ‘yan sanda ba su kama shi ba, ba su kuma tsare shi ba, amma ‘yan sandan sun cece shi ne daga wajen.
Ya ce, an fara bincike a kan lamarin, ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
Majiyarmu ta lura da cewa, yanda Kwamishinan ‘yan sandan Jihar ta Kano, Mohammed Wakil, ya fuskanci sha’anin zaben a lokutan zaben da ma bayansa ya ceto Jihar daga fadawa wani mummunan yamutsin siyasa.
Wakili, wanda ya shahara da yaki da shan miyagun kwayoyi, ya kai ziyara wuraren kada kuri’a masu yawa inda rikici ya so ya barke, ya shawo kan lamurran.
An ma ganshi a cibiyar tattara sakamakon zaben ta karamar hukumar ta Nasarawa, yana sasantawa a tsakanin wakilan jam’iyyu.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa, Auwal Ibrahim, cewa ya yi, Kwamishinan ne ya kawo shawarar a rubuta takardan yarjejeniya a kan zaman lafiya a tsakanin wakilan jam’iyyun da kuma yanda za a warware matsalar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!