Connect with us

KIWON LAFIYA

Yadda A Ke Magance Gajiya Da Kasalar Jiki

Published

on

Silas mai shekaru 50 ya mallaki wani wuri ne wanda ake yin shagulgula daban-daban, yana kuma yin aiki ne kusan ko wacce rana ne, a cikin mako , amma sai watarana ya fadi, aka kuma yi saurin kai shi asibiti.Ya bayyana cewar Likita ya duba shi ya kuma gane cewar yanafama da cutar gajiya, inda kuma ya bashi shawarar ya samu ya huta, ya kuma lura da kan shi sosai.
‘Yarsa Ruth ta bayyana cewar yana da wuya Silas ya ci abinci ko kuma ya yi barci,koda kuwa yana kukan ciwon jiki, ciwon kai da kuma kasala.
“Ya ki yarda ya ajiye aiki saboda yana son shi ya rika yin komai, bayan kuma da akwai wadanda za su yi shi aikin nashi, wani babban abin takaici shine, shi bai zuwa asibiti, lokacin da yake jin alamuncbutar ta gajiya, abin da ya kai ce shi ne ai abin ba wani na damuwa bane, don haka sai ya sayi maganin hana ciwon jiki. Amma sai lokacin daya fadi ne ya “suma” aka yi sauri aka kai shi asibiti,inda Likita ya yi ma shi bayanin cewar ba wata gajiyar da take karama, sai ya fada ma Babana cewar ya rage ayyukan da yake yi, ya samu wadanda za su taimaka ma shi, ya kuma tabbatar da ya samu isasshen hutu, ya kuma guje ma shiga wata matsalar da zata shafi lafiyar shi,saboda kuwa ya san ya fara tsufa, bai kuma da sauran wani karfi sosai wanda zai yi aiki da shi”.
Kamar dai yadda Dokta Ijeawele Osia (psychologist) wanda wani kwararre ne a bangaren halayyar dan Adam, ya bayyana cewar shi ko kuma ita kalmar stress tana nufin rashin daure ma shiga wani hali, na ainihi ko kuma dai haka nan, wanda kuma abin zai iya shafar rayuwar lafiyar hankali, ko jiki, ko abin ya shafi yanayin da shi mutum yake. Ya bayar da misalin stress wanda ya kunshi , kudi, harkar aure ko kuma zama da iyali, wajen aiki, da kuma abubuwan da suka shafi lafiyar mutum.
“Duk dai muna da yadda muke iiyawa da wasu matsalolin da suka shafe mu kamar dai samun canji na wasu al’amura, don haka sanadiyar shiga wani halin damuwa wanda ya kan cutar sannu a hankali, kowa dai yana da dalilan da suka sa shi shiga halin damuwa,, wannan kuma ya bambanta ne daga ko wanne mutum, akwai kuma damuwa mai kyau da kuma mara kyau.”
Ta bayyana cewar ita stress wata hanya da jikin mutum yake iya fuskantar duk wani hali da mutum zai iya shiga, kodai na bukata, ko kuma yin wata barazana.
“ Idan mutum yana tsam mai manin wata matsala na iya tasowa, ko dai ta kasance da gaske ko kuma hakanan dai, sai jiki ya dauki niyyar yin maganin al’amarin, ko dai da gaske ne ; ko kuma hakanan dai, akwai wata kariya ta jiki, wadda take kasancewa cikin shiri na fuskantar shi al’amarin, nan da nan kum abin zai iya kasancewa, wanda kuma wani abu ne wanda ake kira da suna “fight-or-flight” ko kuma matakin mayar da martani .”
“Martanin da ake maidawa na shiga damuwa shine jiki ya kawo wata kariya, idan mutum yana yin aiki kamar yadda ya dace, hakan yana taimakawa wajen mai da hankali, idan kuma ana yinaiki kamar dai yadda ya dace, ga ka kuma ciki kuzari, ana kuma a shirye koma minene zai iya faruwa, wanda ba’a shirya mawa ba., gajiya tana taimakawa wajen kare rayuwa,, da kuma bada wani kuzari wanda yake na daban ne wanda kuma na kare kai ne. Alal misali kamar idan mutum ya fadi kan sitiyari, wannan yana hana hadarin mota. Hakanan ma gajiya tana taimakawa wajen sa mutum ya kasance a shirye saboda ya fuskanci matsaloli, ita kuma ke sawa koda wane lokaci mutum ya kasance yana cikin shirin kota kwana. wato ya kasance zai zama koda yaushe wani sabuwar balaga bayan kuma yana cikin manyan shekaru.
Kada kuma ka bari wani abin da bai da muhimmanci ya dauke ma hankali, kana kokarin ka wasn da baida muhimmanci, ko kuma ka sa kanka yin karatu saboda zaka fuskanci jarabawa, maimakon yanayin naka ya dace da ka kalli Talabijin. Amma sai dfai wani lokaci idan mutum yana cikin halin gajiya, ana iya shiga matsalar damuwa, wadda ta shafi lafiya , yanayin da mutum yake ciki, aikin daya ke yi, irin dangantakar da yake yi ko kuma mu’amala da mutane,sai kuma irin rayuwar da ake yi.
Ita gajiya wata hanya ce wadda jikin mutum yake yin abin da shi jikin yake bukata, wannan kuma yana iya kasancewa a dalilin wasu abubuwan da aka taba fuskanta. ko dai su kasance masu kyau ko kuma akasin hakan. Idan mutane suna jin gajiya wato kamar wani abu yana tafiya a cikin jikinsu da kuma sinadarin, sai jikin su ya nuna wani abu saboda zai saki wasu sinadarai zuwa cikin jin.Su wadannan sinadaran suna bayar da cikakken kuzari da kuma karfi, wanda kuma wani abin so ne, idan ita gajiyar ta danganci hadarin da zai shafi jiki. Amma kuma fa wannan wani abu ne wanda bai da kyau, amma kuma fa idan ita gajiya tana son tayi maganin wani abu wanda yake, ba mai tayar da rai ba, aka kuma yi rashin sa’a babu, ba wani ragowari kuzari, da kuma karfi kamar dai yadda Dokta Osia ta yi bayani.
Kwararrar a bangaren halayen dan Adam ta bayyana cewar abubuwan da suka sa gajiya suna da nasaba da abubuywa masu yawa, wadannan kuma sun hada da jin tsoron wani abu wanda yake da hadari,(kamar damuwa dangane da aikin yi da kuma iyali) gane abin da zai iya ja ma mutum cutar gajiya, wannan ma wata hanya ce akan yadda mutum zai gane shine mutum ya gane yadda iya taikama ma shiId yadda zai samo hanayar da zai yi maganin ita annobar.
Ta bayyana cewar wani abu wanda yake matukar hadari dangane da cutar gajiya shine na yadda yake saukake nakasa al’umma ko kuma mutum, “Ya kamata ace yanzu ka saba da yadda yake, a hankali ana iya sabawa , har ma a samu warkewa. Ba kuma zaka iya gane yadda take damuwar ka ba, wannan shi yasa yana da kyau ka san ko yaya su alamun na cutar take.”Kwararrar ta bayyana cewar su alamun kamuwa da cutar gajiya sun hada da wadanda ake iya lura dasu, sai kuma na jin dadi, wanda ake gani, da kuma ta halayya..
Dokta Osia ta bayyana cewar shi dukkan wasu matsalolin da shafi al’amarin lafiya akan shiga a sanadiyar, basu da wata alaka ko kuma ita gajiya, mutane ya dace su tuntubi Likita ko kuma wani kwararre a halayen dan Adam, sai kumasauran wadanda suka kwararru a ala’amarin daya shafi lafiyar hankali. Wannan kluma sai fa sun ga wasu alamu wadanda aka yi bayani dangane dasu.
Ta bayar da shawarar cewar baya ga bada taimakon magani daga kwararru, ya kamata suma mutane su rika yin wasu abubuwa, domin su kula da yadda ake lura da al’amarin rashin lafiya na cutar gajiya.
•Yin abubuwan da za su taimaka ma kan ka, ka kuma yarda cewar da akwai wasu wuraren da ko kuma wasu shagulgulan da ba sai kaje ba.
• Ka bi a hankali koda yaushe maimakon ka kasance wanda yake tayar da hankal, ka kuma tuna da abubuwanda suke damuwarka, ka kasance koda wanne lokaciu kai mai tawali’u ne, kada kum ka kasance wanda yake saurin yin fushi, ka kare hankalin ka daga duk wani abin da bai da kyau.
•Ka koya da kuma ka rika yin koyon shakatawa ko kuma hutawa, kana kuma iya amfani ne da dabarun yoga ko kuma ko kuma yadda za ‘a yi maganin gajya.
•Rika yawan motsa jikisaboda jikinka zai iya maganin damuwa kamar dai yadda ya dace, sai kuma cin kayayyakin abinci masu nagarta.
•Ka san yadda zaka rarraba lokacin ka kamar yadda ya kamata, ka kuma samu iya mizanin da zaka iya, kada ka kure kanka, ka kuma koyi lokacin da zaka ce kai ba zaka iya ba, akan wasu abubuwan da za su samar maka da damuwa. Ka ware ma al’amarin yin wasu abubuwan da kafi sha’awar yi, yi, da kuma hutawa.
•Ka samu hutawa da kuma barci sosai, saboda jikin ka yana bukatar lokacin da zai samu hutu sabodaa samu mayar da komadar da aka rasa daga can baya.
•Kada ka dogara akan kwayoyin magunguna ko kuma giya, ko kumayin wasu halayen dab basu dace ba, ka samu damar kasancewa tare da wadanda kake jin dadin mu’amala
•A nemi magani daga wuraren kwararru ko kuma wadanda suka ko kuma wadanda al’amuran da suke da nasaba da kula da lafiyar hankali, ko kuma ka koyi hanyoyin da suka kamata na yadda zaka zauna ka lura da gida musamman ita cutar ta gajiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!