Connect with us

SIYASA

Zababben Dan Majalisar Dokoki Ya Sha Alwashin Samar Da Ababen More Rayuwa A Yankinsa

Published

on

Zababben dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar karamar hukumar Rafi, Hon. Abdullahi Magani Gaba ya sha alwashin samar abubuwan more rayuwa a yankunan karkara. Dan majalisar ya bayyana hakan ne jim kadan da bayyana sakamakon zaben da hukumar zabe tayi a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.
Hon. Abdullahi Gaba ya cigaba da cewar na fara neman wannan matsayin nan tun a shekarar 1999 irin halin da na ga jama’ar mu na ciki na rashin cigaba na daga cikin abinda ya tunzura ni neman wakilci a majalisar dokoki na jiha, Allah cikin ikonsa na samu nasarar cin zabe a inuwar APC. Muna bukatar hanya domin akwai dubban manoma da ke fuskantar matsaloli na rashin hanyar da zamu bi wajen kai anfanin gona a manyan kasuwanni.
Yanzu abinda na ke muradin mayar da hankali akansu guda uku ne, wanda ya shafi hanya musamman wanda ya tashi daga kusharki zuwa Tungan Bako, sai samar da makarantun boko dan saukakawa matasan mu samun damar neman ilimin zamani cikin sauki, akwai maganar inganta dakunan shan magani, wato inganta kananan asibitoci a inda ake da su, da samar da karin wasu a inda babu su.
Ina da tabbacin idan aka samu wadannan abubuwan to lallai za a inganta rayukan dubban mutanen da ke zaune a wannan yankin, a karamar hukumar Rafi muna da gundumomin goma sha daya, shekaru ashirin da na yi ina kenfe a wadannan wuraren na fahimci irin kalubalen da suke fuskanta, kan haka na san idan aka samu kulawa ta musamman aka isar a majalisar dokoki kuma suka samu nasarar shiga cikin kasafin kudin gwamnati lallai ne jama’ar mu zasu samu cigaba ta yadda tattalin arzikin mu zai bunkasa.
Matasa da dama sun nuna farin cikin su musamman ganin an samu wannan canjin a lokacin da ya dace. Alhaji Sa’idu Tungan Bako yace sun fara siyasar nan tun 1999 kuma mun raka ‘yan siyasa da dama kuma mun ga gudun ruwan kowa, saboda haka a wannan lokacin muna kyautata zaton zamu iya samun nasarar da muke nema na cigaban al’ummomin mu. Misali duk da irin dubban jama’ar da ke zaune a wannan yankin muna da kuri’u dubbai amma kusan ba ma samun masu yin tsayin daka wajen ganin mun samu sassaucin rayuwa. Amma muna kyautata samuwar Hon. Abdullahi Gaba a majalisar dokokin jiha, za mu iya samun wakilcin da zai taimakawa al’ummar karamar hukumar Rafi cin moriyar mulkin dimukuradiyya da kuma manufofin jam’iyyar APC na inganta rayuwar mutanen karkara ta fuskar ayyukan raya kasa, bunkasa tattalin arzikin kasa ta fuskar noma da kiwo, bunkasa kananan sana’o’in wanda shi ne jigon rayuwar jama’ar mu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!