Connect with us

KASUWANCI

Zirga Zirgar Fasinjojin Jiragen Sama Ya Karu A ‘Yan Kwanakin Nan

Published

on

A bisa adadin da aka samo daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa NCAA sun nuna cewar, yawan jiragen da sukayi zirga-zirga a cikin Nijeriya an samu karin yawan fasinjoji a shekarar 2018.
Adadin wanda wakilinmu ya samo daga gun hukumar ta NCAA a ranar juma’ar data gabata ta nuna cewar, jiragen sun samu 5,420 na zirga-zirgar jiragen takwas a cikin watan Janairu da suka kai yawan 4, 838 na jirage tara a shekarar 2017.
Kamfanin jirgin sama na Air Peace ne ke akan gaba da sauran jiragen, inda yake da yawan zirga-zirgar data kai 2, 129 sai kuma kamfanin jirgi na Arik nada ya yi zirga-zirgar data kai 1, 138 sai kuma kamfanin jirgin Med-Biew yana da mafi karanci da ya kai 87.
A zirga- zirga daga kasa zuwa kasa kamfanin jirgin sama dake Accra na Africa World Airlines ya yi zirga-zirgar data kai 30, inda ya yi zirga-zirgar data kai 152 sai kamfanin jirgi na Air Peace ya yi zirga-zirgar data kai 132 sai kuma kamfanin jirgi na Asky dana Ethiopian Airlines, sunada 107 da kuma 92.
Kamfanin jirgin sama dake a birnin Khartoum a cikin kasar Sudan na Tarco Air, ya samu kasa da zirga-zirgar jirage biyu.
Har ila yau, kamfanin jirgi na Emirates yana da yawan fasinjojin da ya yi jigilar su da suka kai yawan 23,630 da kuma 24,955.
Kamfanin jirgin sama na Emirates ya take baya da yawan fasinjoji sai kuma kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines nada fasinjoji guda 22,653 da kuma fasinjoji guda 24,508.
Acewar kungiyar IATA, a cikin watan janairu yawan fasinjojin ya karu.
Kungiyar ta IATA ta kara da cewar, daga shekara zuwa shekara na fasinnijin da akayi jigilar su sim kai kashi 5.1 bisa dari a cikin watan Janairu.
Acewar kungiyar, wannan karin ci gaba ne idan aka kwatanta data wstan Disambar shekarar 2018 na yawan fasinjojin da sukayi zirga-zirga a nahiyar Afirka.
Kungiyar ta IATA ta kara da cewar, karfin kwarin gwiwar da ake da ita tana raguwa a Nijeriya tun a cikin watan Nuwamba, inda ya ci gaba da kasancewa har kashi 50 idan akayi la’akari da kasar Masar da Afirka ta Kudu
Manajin Darakta na Aglow Abiation Support Serbices Mista Tayo Ojuri ya sanar da cewar, daya daga cikin manyan dalilan na karuwat zirga-zirgar matafiyan shine saboda daukin da aka samar a fannin da kuma samar da kyakyawan yanayi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!