Connect with us

RAHOTANNI

An Daure Wani Mutum Saboda Bugun Ma’aikacin Wutar Lantarki

Published

on

A jiya ne wata kotun shari’ar musulunci na daya dake Unguwan Gwaza, a garin Gusau ta jihar Zamfara ta zartar wa da Habu Mai Shago dake unuguwan ‘Federal Low Cost Housing Estate’ na Tudun wada, Gusau zaman shekara daya a gidan yari a bisa laifin kai hari ga ma’aikacin kamfanin samar da wuta na ‘Kaduna Electric’ a yayin da yake gudanar da ayyukansa.
Alkalin kotun, Alhaji Labaran Salisu, ya samu wanda ake zargin, Malam Habu Mai shago, da laifin hadin baki tare da hana ma’aikacin gwamnati gudana da aikinsa tare da kuma ji masa ciwo a yayin da yake gudanar da ayyukansa, wadanda dukkan su laifi ne a karkashin sashi na 123 da 318 na dokar shari’a ta jihar Zamfara.
An kuma umurci wanda aka yanke wa hukuncin biyan dukan kudaden da wanda aka ji wa ciwon ya kashe a wajen neman magani.
Jami’in ‘yan sanda mai gabatar da karar, Bashir Rabiu, ya bayana wa kotun cewa, wani jami’in ‘yan sanda ne ya kama wanda aka yanke wa hukuncin bayan da hukumar samar da wuta na ‘Kaduna Electric’ suka nemi taimakon ‘yan sanda saboda harin da ya kai wa ma’aikacin amfanin.
Binciken da aka yi ya nuna cewa, Habu Mai Shago ya jagoranci ‘yan iskan dake unguwan (Federal Low Cost) inda suka kai hari ga ma’aikacin a yayin da yake gudanar da ayyukansa, inda suka ji masa ciwo.
Bayan da aka karanto masa laifinsa, Habu Mai Shago ya amince da aikata laifin amma ya nemi kotu ta yi masa ahuwa. A kan haka ne alkalin kotun ya yanke masa hukuncin zama a gidan yari na wata 6 a kan laifukan guda biyu ya kuma bashi zabin biyan Naira dubu 6 in har baya son zaman gidan yarin.
Jami’i mai kula da kaduwanci na kamfanin na yankin Gusau, Injiniya Abdul Sabo, ya yaba wa hukuncin ya kuma bukaci al’umma su guji irin wannan aikin ya kuma yi fatan hukuncin da aka zartar zai zama darasi ga sauran jama’a a nan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!