Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Tsohon Dalibi Da Laifin Sayar Da Kwaya A Edo

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin muyagun kwayoyi ta Jihar Edo, ta cafke wani tsohon dalibin kwalejin kimiya mai suna Lucky Abel, bisa zargin sa da laifin sayar da kwaya. Wanda ake zargin dan asalin Jihar Benuwai ne, kuma an samu nasarar cafke shi ne a Okada cikin karamar hukumar Obia ta arewa maso yamma da ke Jihar. Cikin kwayar da ake zargin yana sayar har da hodar Ibilis da kuma wuwi.
Kwamandar hukumar NDLEA na Jihar Edo, Buba Wakawa, ya tabbatar da wannan kame. Ya bayyana cewa, “An samu nasarar cafke shi ne bisa bayanai da aka samu na cewa, wanda ake zargin yana gudanar da haramtacciyar kasuwanci a Jihar. “A cikin kwayar da aka samu daga hannun wanda ake zargin dai sun hada da sunkin hodar Ibilis guda takwas mai nauyin giram 24, sunkin wiwi guda 53 mai nauyin giram 250 da dai sauran su.”
Wakawa ya bukaci matasa da kuma sauran mutane su daina safarar muyagun kwayoyi domin su samu rayuwa mai inganci. “Safarar muyagun kwayoyi yana hana samun nasara a rayuwa. Wannan mai laifin da aka kama, ya kamata a ce yana cikin ganiyar karatunsa ko kuma wani aiki mai inganci, amma a yanzu hakan zai samu ne idan ya gama fuskantar hukuncin laifin da ya aikata,” in ji shi.
A bayanin wanda ake zargin dai, ya bayyana cewa ya fara safarar muyagun kwayoyi tun a shekarar da ta gabata. Abel ya ce, “Na fara sayar da muyagun kwayoyi tun a shekarar da ta gabata. Na yi makarantar sakandiri a ‘Okada Grammar School’ da ke cikin garin Okada, kuma na kammala a shekarar 2010. Bayan nan, na karanta harkar kasuwanci a kwalejin kimiya na Jihar Edo da ke Usen a shekarar 2013.
“Bayan na samu takardar difloma dina, na nemi aikin da zan yi a rayuwana amma ban samu ba. Ta haka ne abokina ya shigar da ni wannan mummunar aiki na safarar muyagun kwayoyi. Domin in samu riba mai yawa, ina sayar da hodar Ibilis da wiwi da dai sauran su. Ina samun wannan kwaya ne daga New Road da ke cikin karamar hukumar Obia ta kudu maso yamma ta Jihar Edo.”
Kwamandar hukumar NDLEA, ya bayyana cewa za a mika wanda ake zargin zuwa kotu indan an kammala bincike, ya kuma garkadi dilolin muyagun kwoyoyi da su bar wannan mummunar sana’a ko kuma a cafkesu su fuskanci hukunci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!