Connect with us

KASUWANCI

An Yi Kira Ga Babban Bankin Nijeriya Ya Kara Wa NIRSAL Da MFB Bashin Naira Biliyan 100

Published

on

Cibiyar bin tabbatar da yin adalci ta kasa CSJ, ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya CBN da kuma Kwamitin Ma’akata Bankuna dasu daga darajar bashin da ya baiwa kamfanin NIRSAL da kuma ta Bankin Microfinance daga naira biliyan 5 zuwa naira biliyan 100.
NMFB wani sashe na Kwamitin Ma’aikatan Bankunan, inda Kwamitin yake bayar sanya baki wajen bayar da kudin shi kuma ya samu nasa kason da ya kai kashi 50, inda kuma NIRSAL, NIPOST suke samun kashi 40 da kuma kashi goma.
Gwamnan CBN Mista Godwin Emefiele a satin da ya gabata a ran gadin da ya yi zuwa MFB ya bayyana cewar, za a bayar da bashin akan kashi biyar, inda za a biya a cikin shekaru bakwai.
Da yake tsokaci akan maganar a ranar Lahadin data gabata, Darakatan CSJ, Mista Eze Onyekpere ya yi nuni da cewar hakan zai taimaka matuka daga durkushewar matsakaitan kasuwancin daga jarin naira biliyan ga MFB ganin cewar kudin sunyi kadan wajen cike gibin da ake dashi.
Ya kara da cewar, hakan zai kuma taimakawa matakaitan sana’oi magance kalubalen da suke fuskanta.
Ya ce mahummancin shine, kudin ruwan zai zamo baida wani yawa gannin cewar wadanda zasu amafana zasu samu tallafi.
Samun bashi yana ci gaba da zamowa kalubale ga matsskaitan sana’oi a kasar nan kuma wasu bankunan kasuwanci basu son su bayar da bashi ga masu matsakaitan sana’oi.
Acewar sa, Shiyar naira biliyan biyar ta yi kadan sosai domin a kalla ana bukatar shiyar naira biliyan 100, unda ya kara da cewar, un kuma aka kaiwa Bankunan Micro dauki zai kara karafafa ayyukan su da kuma kara gasa a tsakanin takwarorin su.
Ya yi nuni da cewar kirkirar zata kuma taimaka wajen samar da ayyukan yi ga yan kasar nan kuma matsakaitun sana’oi zasu uya samun sukunin samun bashi.
Onyekpere ya bayyana cewsr, kafa MFB zai taimaka wajen samun riba ga masu matsakaitan sana’oi dake kasar nan da kuma dai-daikun yan kasuwa yadda suma zasu dinga habaka kudin shigar gwamnati.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!