Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Jajantawa Iyalan Daliban Da Suka Mutu A Legas

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar ruftawar wani bene a jihar Legas.

Ana fargabar cewa dalibai da dama sun mutu, yayin da ginin wata makaranta ya rufto a kansu a birnin Legas da ke Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.

Har ila yau, shugaban ya bukaci gwamnatin jihar da dauki matakan da suka dace wajen kiyaye faruwar hakan a nan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!