Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

EFCC Ta Kama Wata Mata Da Laifin Zambar Miliyan 21

Published

on

A ranar Talata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da wata mata mai suna Jallaba Mala Bukar, a gaban babban kotun Maiduguri, bisa laifin zambar naira miliyan 21.9 na zuba jari. An gurfanar da Bukar ne a gaban alkali mai shari’a Abdullahi Sanya na babban kotun Jihar Borno wacce ke da zama a Maiduguri, bisa laifuka guda uku wanda suka hada da damfara.
Hukumar EFCC ta gurfanar da wacce ake hukuma ne bayan gudanar da binciken kararraki guda uku a kan ta, wadanda suka bayyana cewa a cikin shekarar 2017, a lokuta daban-daban ana zargin ta damfari Mohammad Nur Alhaji da Hafsat Muhammad da kuma Bana Modu wadanda suka amince da ita wajen ba ta kudadesu domin ta saya musu hannun jari a kamfaninta mai suna Swithgolden.
Ana tuhumar Bukar ne a kan kudaden da aka ba ta domin ta sayi hannun jari da su ne, amma sai ta yi amfani da kudaden wajen bukatun kanta, duk kokarin da aka yi domin ta maida kudade amma lamarin ya ci tura.
Bukar ta musanta laifin da ake tuhuman ta da shi.
Lauya mai gabatar da kara Haruna Abdulkadir, ya bukaci kotu ta saka wata rana na sake sauraran karan.
Alkali mai shari’a Sanya ya dage sauraran wannan kara har sai ranar 2 da 3 da kuna 4 ga watan Afrailun shekarar 2019, domin sake saurarar shari’ar, sannan kuma ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wacce ake tuhuna a gidan yari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!