Connect with us

KIMIYYA

Facebook Sun Gamu Da Gagarumar Matsala  A Tarihinsu

Published

on

Rahotanni daga kafafen watsa labarai sun bayyana cewa; Kamfanin shafin Facebook na fuskantar matsala mafi tsanani a tarihinsa, inda ake cin karo da matsaloli wajen aiki da wasu daga cikin manhajojinsa na Intanet a fadin duniya.

Sai dai kamfanin ya ce yana kokarin shawo kan matsalar. Baya ga ainihin shafin na Facebook shi kansa, manhajar Messenger da Instagram su ma sun gamu da cikas.

Ba a dai gano abin da ke haddasa matsalar ba, wadda ta fara tun kusan karfe hudu na yamma agogon GMT, wato biyar na yammacin jiya a gogon Nijeriya da Nijar.

LEADERSHIP HAUSA A YAU ta lura da yadda masu amfani da sahar na Facebook suna iya bude shafin, amma kuma ba sa iya sanya abubuwa da suka bukaci su saka a shafin musamman inda yana dauke da hoto sakon da kake son turawa din.

Manhajar ‘Messenger’ wanda yake mallakin ‘Facebook’ din ne da yake aiki a waya tana aiki ga wadansu amma kuma wadansu ba ta yi musu aiki, sai dai kuma manhajar ta Kwamfuta ba ma a samunta.

Rahotanni sun nuna cewa; matsalar dai ba ta shafi WhatsApp ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!