Connect with us

SIYASA

Farfesa Zulum Ya Mika Sakon Godiyar Sa Ga Al’ummar Borno

Published

on

Zababben gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana godiyar sa ga al’ummar jihar, bisa damar da suka bashi wajen jagorantar ragamar su, musamman wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kaiwa ga nasarar zaben sa a matsayin gwamnan jihar.
Haka zalika kuma, ya dauki alkawari wajen yin aiki tukuru a ci gaba da sake bunkasa ayyukan ci gaban da Gwamna Kashim Shettima ya fara, a fadin jihar Borno.
“wanda bisa ga wannan ne zan kara tabbatar wa baki dayan al’ummar jihar Borno kan cewa, bisa ga wannan babban nauyi wanda kuka damka mini. Wanda kuma in sha Allah zan yi iya kokarina wajen ci gaba da bunkasa wa da kyautata ayyukan da Gwamna Kashim Shettima ya fara; wadanda suka kunshi sake gina yankunan da matsalar tsaro ta shafa”.
Har wa yau kuma, ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta yi kokari wajen kyautatuwar sha’anin tsaron jama’a tare da dukiyoyin su- lamarin da shi ne nauyin da ya hau kan kowacce gwamnati, ta kare rayukan yan kasa da dukiyar su.
Haka kuma, Farfesa Zulum ya sha alwashin mayar da hankali wajen lalabo ingantattun matakan bunkasa masana’antu da cibiyoyin tattalin arzikin jihar Borno, ta hanyar baiwa matasa horo na musamman, wanda zai taimaka domin kirkiro da ayyukan yi a tsakanin matasan.
Bugu da kari kuma, ya yi alkawarin kara kaimi wajen bunkasa sha’anin kiwon lafiya tare da kyautata bangaren ilimi da farfado da lamurran ayyukan noma, domin samar da karin hanyoyin zaburar da ci gaban jama’ar jihar.
“Har wala yau kuma, na yi imani kan cewa a duk lokacin da mutum ya kuduri aniyar ci gaba, matukar hakan ya zauna a zuciyar sa, gano hanyoyin da zai bi, ba zai bashi wahala ba. A matsayin mu wadanda nauyin sake gina jihar Borno yake a wuyan mu- ina nufin kowanne dan jihar Borno”.
“kuma a bisa ga hakan ne, ina da matukar burin yin aiki da kowa da kowa, ciki kuwa har da wadanda suka yi takara tare dani. Saboda na yi imani kan cewa, aiki wuri guda shi ne mafi muhimmanci da kalubalantar juna”. Inji shi.
A hannu guda kuma, zababben gwamnan ya yi kira na bai daya ga daukwacin al’ummar jihar Borno, su taru wuri guda wajen yin aiki tukuru domin cimma nasarorin gwamnatin sa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!