Connect with us

RAHOTANNI

Jama’a Na Ci Gaba Da Zanga-Zanga A Bauchi Kan Kin Ayyana Sakamakon Zaben Bauchi

Published

on

Dandazon jama’a daga cikin jihar Bauchi sun yi ta hawa kan titina daban-daban na jihar suna masu bayyana bukatarsu ga INEC da ta gaggauta bayyana wanda ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar domin kauce wa tashin hankali da fitinin da rashin hakan ka iya hawo wa jihar.
Wakilinmu ya shaida cewar masu zanga-zangar sun kara yawa da karfi ne a jiya Labara, inda suka hau kan titunan jihar dauke da kwalayen da ke shaida bukatunsu na kiran a bayyana wanda ya lashe kujerar ta gwamna, gabanin nan sun gudanar da addu’o’i na musamman domin cimma burinsu.
Bayan da masu zanga-zangar suna yi macin a wasu sassan jihar, sun kuma mamaye ofishin ‘yan jaridu da ke Bauchi domin shaida wa ‘yan jaridun bukatunsu da abun da suke so cikin gaggawa, masu zanga-zangar ta lumana sun kwashe tsawon awanni suna bayyana bukatunsu.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da muka zanta da su, sun shaida cewar babban barazanar da suke fuskanta shine yunkurin yin rashin adalci da kuma barazanar da jihar take fuskanta na tashin hankali da zarar aka hana wanda ya samu nasara damarsa ta zama gwamnan jihar.
Daya daga cikin masu zanga-zangar Sulamai Mai Fosta, ya shaida cewar, “Abun da muke so kawai shine a sanar da wanda ya samu nasara cikin gaggawa, sannan, duk wani yunkurin da gwamnati mai ci take yi na magudi lokaci ya kure mata, an yi zaben nan lafiya, muna zaune lafiya a jihar Bauchi don haka ba mu son duk wani abu da zai jawo tashin hankalin jama’an jihar ta Bauchi.

“Muna kira ga shugaban hukumar zabe na kasa ya tashi tsaye wajen tabbatar da bayyana wanda ya samu nasara kuma shine Dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir,” A cewarsa, yin hakan zai taimaka wajen kyautata zaman lafiya a jihar.
Wani daga cikin masu zanga-zangar daban, ya kuma ce, “ba za mu jira wani ranar sake yin zabe ba, domin tunin ma wanda ya samu nasara ya rigaya ya lashe kujerarsa, abun da muke jira kawai a ayyana Kauran Bauchi a matsayin sabon gwamnan jihar Bauchi,” Inji shi.
Hajiya Adamu Miri ta ce, dukkanin matsalolin da suka rashin bayyana sakamakon gwamnan jihar ya janyo za su daura ne wa hukumar zabe da gwamnatin jiyar da ke mulki a yau, don haka ne ta nemi INEC ta duba zaman lafiyar jihar da jama’an jihar ta ayyana Sanata Bala a matsayin sabon gwamnan jihar. ta ce, a matsayinsu na uwa mata suna cike da damuwa kan lafiya da rayukan ‘ya’yansu don haka sune bidar zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar.

Ita kuma Madam Rhoda Jibrin Y.D shugaban kungiyar ‘Bauchi State Concern Citizen’, ta shaida cewar babu wani dalilin kin bayyana wanda ya samu nasara, ta bukaci kungiyoyi da al’umman jihar Bauchi da su fito su gudanar da zanga-zangar lumana domin bayyana wa duniya bukatar jama’an jihar Bauchi na a baiwa wanda ya samu nasarar lashe kujerar cikakken damarsa na zama gwamnan jihar.

Wakilinmu da ke Bauchi ya shaida mana cewar masu zanga-zangar dai sun kunshi maza da mata, ciki kuwa har da tsofi, inda suka kuma yi yunkurin kutsa kai zuwa ofishin hukumar zabe da ke Bauchi INEC amma jami’an tsaro sun ki barinsu su tsalleke shingayen da aka sanya domin baiwa ofishin na INEC din kariya.
LEADERSHIP AYAU ta nakalto cewar masu neman a bayyana sabon gwamnan jihar, sun gudanar da addu’o’i na musamman domin cimma burinsu na ganin a bayyana Kaura a matsayin sabon gwamna, masu addu’ar sun hallara a filin Idi na jihar inda suka roki Allah kan bukatunsu. kana sun gangaro zuwa manyan da kananan titunan jihar suna masu gudanar da zanga-zangar lumana domin a bayyana musu wanda ya ci.

A gefe guda kuma, jami’an tsaro na ‘yan sanda sun tsaya a gefe suna kallon masu gudanar da zanga-zangar domin tabbatar da komai na tafiya bisa tsari, kawo lokacin da wakilinmu ke aiko da rahoton nan babu wani labarin tashin hankali da aka samu a sakamakon zanga-zangar, sai dai masu zanga-zangar sun sha alwashin cewar za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar muddin ba a ayyana wanda ya lashe kujerar cikin hanzari ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!