Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Dan Wasan Da Arsenal Take Nema A Roma?

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana nazarin neman dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Roma dake kasar Italiya, Under Cengiz a kakar wasa mai zuwa a kokarin da kungiyar takeyi na kara karfin ‘yan wasanta na gaba.
Hukumomi a kungiyar ta Arsenal dai sun bawa kociyan kungiyar, Unai Emery, fam miliyan 40 kacal domin siyan sababbin ‘yan wasa wanda hakan yake nufin akwai bukatar kociyan yayi kokari wajen sanin kalar ‘yan wasan da zai siya saboda rashin isassun kudi.
Wasu rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa Arsenal ta dade tana zawarcin dan wasan tun a kakar wasan data gabata zuwa watan Janairun daya gabata kafin dan wasan yatafi jinya watanni biyu da suka gabata.
Duk da cewa dan wasan baya samun wasanni akai-akai tun acikin watan Janairu amma kociyan kungiyar yana fatan ganin ya siyi dan wasan domin kara karfin ‘yan wasansa na gaba duk da cewa kawo yanzu kungiyar tanada manyan ‘yan wasan gaba.
Under Cengiz dan shekara 21 a duniya kuma dan kasar Turkiyya yafara bugawa kungiyar Roma wasa tun yana matashi dan shekara 19 kuma kungiyoyi da dama suna zawarcin dan wasan da suka hada da Tottenham da Atletico Madrid.
Har ila yau Arsenal ta tura wakilanta domin zuwa kasar Italiya su kalli yadda dan wasa Suso na AC Milan yake buga wasansa bayan da wasu rahotanni suka bayyana cewa idan basu samu damar siyan Under Cengiz ba Suso zasu nema.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!