Connect with us

RAHOTANNI

Kotu Ta Nemi Mutum Ya Nemo Wanda Ya Tsayawa A Shari’a Ko Ta Daure Shi

Published

on

A ranar Litinin ne babban kotun Jihar Legas wacce take zaune a Igbosere, ta umurci Nurudeen Ekundayo, wanda ya tsayawa wani dan kasar Burtaniya wanda ake tuhuma da laifin damfarar naira miliyan 10.32 mai suna Syed Kamran, ko dai ya bayyana wanda ake tuhuma ko kuma ya yi sirin zuwa gidan yari.
Alkali mai shari’a ya gargadi Ekundayo, wanda bai halacci zaman kotun ba sakamakon rashin lafiya, zai kasance a gidan yari idan bai bayyana wanda ya tsaya mashi ba.
‘Yan sanda sun gurfanar da Kamran ne a gaban kotun Ogba a shekarar 2015, bisa zargin sa da laifin damfarar ‘yan Nijeriya guda 11 naira miliyan 120. Lauya mai gabatar da kara ya zargi Kamran amsar kudade daga hannun mutanen domin ya kawo musu mai fetur, amma sai ya ki kawowa.
Dan kasar Birtaniyan wanda ya kwashe tsawan watanni a gidan yari sakamakon rashin samun beli, ya tsare ne daga masaukinsa lokacin da aka sake shi. An bayyana cewa, ‘yan sanda sun sake cafke Kamran a filin jirgin saman Mrtala Muhammed da ke Jihar Legas, lokacin da yake kokarin fecewa zuwa kasar Burtaniya.
An sake gurfanar da shi a gaban alkali mai shari’a Modupe Nicole-Clay, a shekarar 2016, bisa laifuka guda biyu wanda suka hada da, hada kai domin aikata laifi da kuma laifin damfarar naira miliyan 10.32 na wani basarake a Jihar Imo mai suna Ubochi .C. Ubochi.
A cewar lauya mai gabatar da kara, wanda ake tuhuma ya aikata wannan laifin damfarar ne tare da hadin kan kamfanin mai fetur na boji.
Ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi, inda ya bukaci a bayar da belinsa. Lokacin da Kamran bai halacci zaman kotun ba, sai alkali mai shari’a ya umurci a kawo wanda ya tsaya masa wato Ekundayo.
A ranar Litinin ne aka ci gaba da zaman kotun, dama alkali mai shari’a Nicole-Clay ya bai wa wanda ya tsamasa ranar 21 ga watan Junairu, ya bayyana Kamran ko kuma ya yi shirin zama a gidan yari.
An kara dage ranar bayyanar wanda ake tuhuma ne lokacin da lauya mai kare wanda ya tsaya masa, O. Adeniyi ya bukaci a kara masa lokaci. Adeniyi ya bayyana wa kotu cewa, wanda yake karewa ba shi da lafiya kuma har an kwantar da shi a babbar asibiti. Adeniyi ya bukaci a dage shari’ar har wanda yake karewa ya samu sauki. “Shari’ar ce ta saka wanda ya tsaya masa ya samu hawan jini . Shi da dan kasar Burtaniyar sun hadu ne a wurin rawa inda a nan ne suka zama abokai,” in ji shi.
A hukuncinsa, alkali mai shari’a Nicole-Clay ya bayyana cewa, “Wanda ya tsayawa wannan dan Burtaniyan yana da zabi uku, ko dai ya bayyana wanda ake tuhuma, ko ya kawo takardar belinsa ko kuma ya yi shirin zaman a gidan yari na tsawan lokacin da za a yanke wa wanda ake tuhuma. Rahoton asibiti ya nuna cewa, ya kamu da hawan jini. Duk wannan ba zai hana shi halattar zaman kotu ba.”
An dage sauraran shari’ar har sai zuwa ranar 24 ga watan Yuli.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!