Connect with us

KASASHEN WAJE

Kotun Kasar Ostireliya Ta Daure Tsohon Limamin Coci

Published

on

Wata Kotu a kasar Australiya ta yanke hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari kan wani tsohon babban limamin coci, Cardinal George Pell da aka samu da laifin lalata da wasu yara biyu dake aiki a cocin.

Cardinal Pell wanda shi ne tsohon mutum na uku a jerin shugabannin mabiya Darikar Katolika dake fadar Vatican, wanda ke kula da baitulmali, kana kuma ya taimaka wajen zabo Fafaroma guda biyu, ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 1996 zuwa 1997.

Alkalin kotun, Peter Kidd ya bayyana halayen Cardinal Pell mai shekaru 77 a matsayin abin takaici da kuma Allah wadai saboda kimarsa da mukamin da ya rike.

Cardinal Pell mai shekaru 77 ya ce zai daukaka kara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!