Connect with us

LABARAI

Majalisa Ta Fara Zama Kan Kasafin Kudin 2019

Published

on

A jiya Laraba ne ‘yan Majalisar Dattijai suka dauki awanni suna tattauna ka’idojin da za su yi amfani da shi wajen tattauna daftarin kasafin kudin shekarar 2019.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya gabatarwa da hadadiyyar zaman majalisar kasa daftarin kasafin kudin a ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 2018.
Bayanin kasafin kudin ya muna cewa, kashi uku na kasafin zai tafi ne a wajen biyan basussukan da ake bin kasar nan, kwatan kasafin kudin kuma ya kama Naira Tiriliyan 2.14, yayin da manyan ayyuka zai ci Naira Tiliyan 2.031.
Cikakken bayanin kasafin kudin ya kuma nuna cewa, za a kashe Naira Tiriliyan 4.04 wajen ayyukan yau da kullum, haka kuma kudaden da za a yi zirga zirga a tsakanin al’umma ya kai Naira Tiriliyan 492.36 za kuma a kashe Naira Biliyan 120 wajen harkokin gwamnati, za kuma a kashe Naira Tiriliyan 2.031 a bangren manyan ayyuka na musamman.
An kiyasta kasafin kudin ne a kan hangen sayar da gangan mai daya a kan Dala 60 da kuma kiyasin hako ganga Miliyan 2.3 na danyen man fetur a kullum, ana kuma sa ran canja Dala daya a kan 305.

Bayani ya kuma nuna cewa, bangaren majalisar wakilai ta zartar da mataki na biyu na kasafin kudin a ranar 29 ga watan Janairu yayin da kuma ita majalisar dattijai ta shirya amfani da kwana biyu don tattaunawa tare da amincewa da daftarin kasafin kudin, an shirya amfani da ranar Laraba da Alhamis don yi wannan tattaunawar, kafin su zartar da kasafin kudin.
A rana ta farko da aka ayyana don tattaunawar, mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu ya ce, ya kamata a gargadi gwamnati a kan shirin ciwo bashi daga kasashen waje.
“Ya kamata mu gargadi kanmu a kan cin bashi don gudanar da manyan ayyuka, ya kamata mu nemo wasu hanyoyin samar da kudade don gudanar da ayyukan, bai kamata mu sayar da rayuwar iyalanmu ba masu zuwa nan gaba.” inji shi.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta shirya mayar da shekarar kasafin kudi zuwa watan Janairu zuwa watan Disamba na kowanne shekara, kama dai yadda yake a shekarun baya.
Wannan matsaya na Ike Ekweremadu ya samu suka daga mataimakin jagoran majalisa, Sanata Ibn Na’Allah, wanda ya ce, har yanzu kasar nan bata kure ka’idar ta na cin bashi ba.
“In aka lura da yawan al’ummar mu da yawan dukiyar kasar nan, masana za su bayana maka cewa, har yanzu bamu kure ka’idar cin bashin mu ba,” inji shi.
A nasa gudummawar, Sanata Shehu Sani dan jam’iyyar PRP daga jihar Kaduna, ya yaba wa gwamnatin tarayya a kan yadda ta ware Naira Biliyan 500 don tallafa wa al’umma ta hanyar shirin nan na ‘Social Interbention Programme (SIP)’ ya kuma yi kira da a gudanar da binciken yadda aka gudanar da shirin a shekarar da ta gabata.
Cikin wadanda suka yi jawabi sun bukaci kwamitocin majalisar su gaggauta tattauanawa a kan lamarin kasafin kudin don a samu zartarwa a kan lokaci.
Za a ci gaba da tattaunawa a kan kasafin kudin a ranar Talata mai zuwa a ranar da majalisar za ta dawo don ci gaba da zaman ta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!