Connect with us

WASANNI

Manchester United Da Liverpool Suna Zawarcin Dan Wasa Tagliafico

Published

on

Kungiyoyin Manchester United da Liverpool sun shiga zawarcin dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Nicolas Taglifiaco wanda tauraruwarsa take haskawa a kungiyar a wannan kakar wasan.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana zawarcin dan wasan bayan a kokarin da takeyi na cike gurbin bangaren hagu na ‘yan wasan bayan ta duk da cewa akwai ‘yan wasa biyu wadanda suke buga wannan bangare.
Sai dai har ila yau ba kungiyoyin Manchester United da Liverpool da Arsenal bane kadai suke zawarcin dan wasan itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta nuna sha’awarta ta siyan dan wasan bayan.
Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ma tana zawarcin dan wasan dan kasar Argentina sai dai a kwanakin baya wakilin dan wasan ya bayyana cewa dan wasan zai iya maye gurbin Marcelo na Real Madrid wanda ake kyautata zaton zai koma Juventus.
A kwanakin baya dan wasan da kansa ya bayyana cewa yana fatan watarana ya buga wasa a gasar laliga sai dai hakan bai hana kungiyoyin gasar firimiyar cigaba da nemansa ba idan har kungiyarsa za ta siyar dashi.
Taglifiaco dai yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka buga wasa da Real Madrid suka samu nasara akansu daci 4-1 har gida a gasar cin kofin zakarun turai kuma kawo yanzu yana daya daga cikin wadanda tauraruwarsu take haskawa a duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!