Connect with us

LABARAI

Osinbajo Ya Gana Da Gwamnonin Bauci Da Adamawa 

Published

on

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kada da gwamnonin jihar Bauci da na Adamawa, ya gana da mutanen biyu ne a lokuta daban-daban, kuma ganawar an yi ta ne a sirrance.

Dukkan gwamnonin biyu suna fuskantar babban kalubale daga zaben da aka gabatar a ranar 9 ga watan Maris din nan da muke ciki, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana zabukkan jihohin shida a matsayin wadanda basu kammala ba, cikin harda na Bauci da Adamawa.

Dukkan gwamnonin biyu basu ce ma manema labarai komai bayan kammala tattaunawar, ranar 23 ga watan Maris ne za a sake gudanar da zabukka a wasu yankuna na jihohi shidan da aka bayyana zabukkansu a matsayin wanda bai kammala ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!