Connect with us

WASANNI

Saboda Cin Kwallaye Juventus Suka Siye Ni –Ronaldo

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa daman saboda ya dinga zura kwallaye a irin wadannan wasannin kungiyar Juventus ta kashe makudan kudade domin siyansa.
A wasan farko da suka buga a kasar Sipaniya dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ce tasamu nasara akan Jubentus daci 2-0 a sati biyu da suka gabata kuma hakan yake nufin Juventus tana bukatar taci kwallaye uku babu ko daya idan har tana son ta tsallake zuwa zagaye na gaba.
Kafin wasan dai kwallo daya Ronaldo kawai ya jefa a gasar ta bana akan tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United sai a ranar Talata inda ya jefa kwallaye uku a ragar wakilan kasar Sipaniya wanda hakan yake nufin sunyi waje da Atletico din.
“Wannan wata rana ce ta musamman ga duk wani dan Juventus saboda munyi bajinta sosai sai dai daman dalilin dayasa wannan kungiya ta kashe kudi ta siyeni shine saboda irin wannan wasan mai muhimmanci” in ji Ronaldo.
Yaci gaba da cewa “Atletico Madrid kungiya ce mai wahalar gaske saboda nasansu sosai kuma suna da manyan ‘yan wasan da zasu iya samun nasara a kowanne yanayi amma kuma mun nuna musu cewa mune Jubentus kuma muna fatan samun nasara a gaba”
Ronaldo wanda ya lashe kofin zakarun turai sau biyar a tarihi guda hudu a Real Madrid sai kuma daya a Manchester United ya zura kwallaye 24 cikin wasanni 36 daya bugawa Juventus a wannan kakar ta bana.
A gobe Juma’a ne dai hukumar kwallon kwallon kafa ta nahiyar turai za ta sake raba kungiyoyi takwas da zasu rage a gasar ta bana wadda za’a buga wasan karshe a filin wasa na Wanda dake kasar Sipaniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!