Connect with us

LABARAI

Wannan Karon Za A Samar Da Majalisar Dattawa Mai Son Ci Gaba –Shugaban Masu Rinjaye

Published

on

A jiya ne Shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan, ya ce zamanin nuna rashin jituwa a maimakon nuna jituwa da neman ci gaba a majalisar Dattawa ya kare a wacan majalisar ta 8.
Sabuwar majalisar ta 9 wacce za a kaddamar a ranar Litini 10 ga watan Yuni, 2019, Lawan ya ce, za ta fara ne a sabon shafi da kuma sabuwar mahanga ta siyasa.
Lawan ya yi wadannan kalaman ne a ranar Talata, sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a kan abin da ‘yan Nijeriya za su tsammata a sabuwar majalisar ta 9, ya ce za ta kasance majalisa ce wacce za ta rika hange a bisa mahangar gwamnati, musamman fadar shugaban kasa.
A cewar shi, “Kasantuwar majalisa ce da mafiya yawan wakilan cikinta za su kasance ‘ya’yan jam’iyyar APC ne, za su rika tafiya tare ne da sashen gwamnati a kan harkokin tafiyar da kasa ba bisa kiyayya ba.
Lawan wanda shi ne dan takaran APC din a kan shugabancin majalisar dattawan a 2015, yana daga cikin wadanda ake gani a sahun gaba na samun shugabancin majalisar a wannan karon na 9, ya bayyana cewa sabuwar majalisar za ta kasance a damfare take da sashen shugaban kasa.
“Fatan mu dai shi ne, a samu karuwan farashin man fetur a kasuwannin Duniya fiye da yanda yake a halin yanzun.
“Magana guda dai ita ce, sabuwar majalisar dattawa ta 9, har ma da sabuwar majalisar wakilai ta kasa ta 9, za su kasance ne a shafi guda tare da sashen shugaban kasa a tsarin mataki na gaba, wanda hakan zai sanya tafiyar ta yi sauki.”
A halin yanzun dai, Jam’iyyar ta APC tana da akalla wakilai 65 yayin da PDP ke da wakilai 41 a cikin sabuwar majalisar ta dattawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!