Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Fashi Sun Kashe Mai Tsaron Shago A Legas

Published

on

An bayar da rahoton cewa wasu ‘yan fashi da makami su hudu sun yi wa mai tsaron shago fashi a Abule cikin yankin Elepe da ke Ikorodu ta Jihar Legas, da misalin karfe 9.48 na daren Lahadi. Mai tsaron shago mai suna Nduka Nwagbala dan shekara 15 daga Jihar Ebonyi, an bayyana cewa an harbe shi ne a hannusa.
Dan’uwansa mai shagon, an bayyana cewa ya yi tafiya zuwa Jihar Ebonyi, lokacin da lamarin ya auku, an kai matashin zuwa asibiti domin yin jinya. Tawagar ‘yan fashin guda hudu sun harbe shi ne lokacin da suka zo yin fashi a shagon.
Wani da lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suuna Ndubuisi ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne kamar dai wasan kwai-kwayo, ya fi zuwa shagon domin ya sayi wasu kayayyaki, sai ‘yan fashin suka umurce shi tare da mai tsaron shagon a kan su kwanta kasa. Ya kara da cewa, ‘yan fashi sun amshe kudaden duka wanda yake so ya sayi kayayyaki a shagon.
A cewarsa, wasu mazauna yankin wadanda suka ga ‘yan fashin sun kira ‘yan sanda, amma sai dai ‘yan sandar ba sui so wurin kan lokaci ba. Ndubuisi ya ce, “Na tafi shagon dan’uwana domin in sayi wasu kayayyaki, kasa da minti biyu da zuwa na shagon, sai wasu matasa suka isa warin.
“Da farfo mun dauka za su sayi wani abu ne. Daya daga cikin su ya fito da bindiga inda bukaci mu ba su hadin kai. Ba mu fahimta ba a lokacin. Domin haka, sai Nwagbala ya ce musu bai fahimci abin da suke nufi a kan mu ba su hadin kai. Sai suka harbi Nwagbala tare da bayyana cewa ba su zo shagon domin su yi wasa ba.
“Daya daga cikin su ya dako karamar bindiga daga aljihun wandansa ina ya harbi Nwagbala a hannunsa. Sun umurce mu a kan mu kwanta kasa tare da mika musa kudin da ke jikinmu bayan sun kammala tattara kudin shagon. “Mazauna yanki sun kira ‘yan sanda lokacin da suka fahimci lamarin. ‘Yan sanda ba su iso wurin a kan lokaci ba.”
Wani mazaunin yankin mai suna Bayo ya bayyana cewa, lokacin da ya samu labarin ‘yan fashin, cikin gaggawa ya sanarwa wani mazaunin yankin wanda yake da lambar ‘yan sanda. Ya ce, an sanarwa ‘yan sanda, amma abin mamaki ‘yan sanda ba su zo wurin ba har sai da suka kammala wannan fashi. Bayo ya kara da cewa, ‘yan fashi ba kasafai suke zuwa wannan yankin ba, amma bin mamaki sai ga shi sun zo ranar Lahadi, lallai wadannan ‘yan fashi sun samu bayani a kan yankin kafin su zo.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar, DSP Elkana Bala, ya bayyana cewa, duk mutanen da suke ikirarin sun kira ‘yan sanda a lokacin, ba su kira lambar ba da agajin gaggawa na ‘yan sanda ba, kawai sun kira abokansu dan sanda ne. Ya ce, “Sun kira wayar abokansu ‘yan sanda ne wadanda suka sani, su kira lambar bayar da agajin gaggawa? Su daina ikirarin sun kira ‘yan sanda idan sun kira wani wanda baya cikin aiki domin ba zai iya yin komi ba, domin ba huruminsa ba ne ya amsa musu nan take. Wasu daga cikin su an canza musu wurin aiki a kan ina suka san su.
“Amma da a ce mazauna yankin sun kira lambar bayar da agajin gaggawarmu, da sun samu taimako cikin gaggawa.”
Ya yi alkawarin zai tuntubi wakilinmu idan ya kammala bincike, amma bai tuntube shi ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!