Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jami’in Gwamnatin Kuros Riba

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Kuros Riba ta bayyana cewa, ta dakile yunkurin sace mai bai wa gwamna shawara ta fannin tsaro, Mista Ani Esin, kamfanin dillancin labarai na kasa ne ya ruwaito wannan labara. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Irene Ugbo, ita ta tabbatar da hakan a garin Kalaba ranar Talata.
Ugbo ta bayyana cewa, daya daga cikin wadanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne ya mutu lokacin da yake yunkurin gudu da motar da suka dauka daga gidan Esin. Ta kara da cewa, ‘yan bindigan sun mamaye gidan Esin da niyyar su yi garkuwa da shi da misalin karfe 3 na dare, amma tawagar ‘yan sanda wanda kwamishinan ‘yan sandar Jihar Mista Austin Agbonlahor, yake jaoranta suka hana su.
Ugbo ta ce, “Daya daga cikin ‘yan bindigan ya mutu lokacin da yake kokarin guduwa da motar da suka dauka daga gidan Esin. “Mun ceto shi sannan kuma a halin yanzu yana cikin koshin lafiya a asibiti.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!