Connect with us

LABARAI

Zaben 2019 Daidai Ya Ke Da Wasan Barkwanci – Falana

Published

on

Shaharraren lauyan nan dan rajin kare hakkin bil adam, Femi Falana (SAN) ya ce, zaben da aka gudanar kwanan nan tamkar wasan kwaikwayo ne.
Falana na magana ne a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin din ‘Channels Telebision’’ ya bukaci yan Nijeriya su hada kansu tare da neman a gudanar masu da sahihin zabe, su kuma tsayu a kan haka.
“Nijeriya ta kashe Naira Biliyan 250 daga kudaden al’umma haka kuma yana zuwa ne bayan da abubuwan da gwamnonin suka kashe wanda ya kai fiye da Naira Biliyan 250.”
“Idan muna bukatar fita daga wannan matsalar dole mu koma mu sake tsari, abin ya wuce lamarin manyan jam’iyyu nan guda biyu, dole Nijeriya ta shiya sahihin zabe fiye da irin wannan wasan kwaikwayon.”
A kan tashe tashen hankulan da aka samu a wasu bangaren kasar nan, Falana ya yi imanin cewa, duk da wa’azin da ake yi tashin hankali a kan harka zabe ba za a iya maganin tashin hankalin da ake samu ba har sai an inganta bangaren shari’a da kuma cibiyoyin kare hakkin bil adam don su tabbatar da an hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin tayar da hankali a lokuttan siyasa da kuma gudanar da zabe.
“Muna da matasa fiye da Miliyan 40 kuma yawancinsu na yawo ne a kan titunan mu ba tare da aikin yi ba, a kan haka in har zaka kwana kana wa’azi baa bin da zai hana matasa fada wa harkokin tashin hankalin siyasa da sauran aikata laiffuka.”
“Dukkan wadanda ake kama wa a laifin tayar da hankali a wajen zabe wakilai ne na manya yan siyasa. Yan sanda da sauran jami’an tsaro sun tabbatar da kama fiye da mutum 200, menene muka yi da wadanda aka kama, abin dake faruwa shi ne da zaran an kammala zabe sai hankalinmu ya kuma koma wani wurin ba tare da mun tabbatar da an hukunta su ba.”
“Ya kamata kotunan zabe su ci gaba da hukunta masu laifukan zabe kamar dai yadda hukumar EFCC da ICPC suke gudanar da binciken lamarin da ya shafi cin hanci da rashawa, amma sai aka yi watsi da wannna shawarar.”
“A bangaren kungiyar masu kare hakkin bil adam, muna shirin hada hanun da INEC don samar da lauyoyi matasa da za su ci gaba da neman a hukunta masu laifin zabe a madadin hukuma zabe ta INEC, in ba aka aka yi ba, haka lamarin zai wuce ba tare da an hukunta kowa ba.”
Falana ya kuma bayyana cewa, za a samu matsala tattare da jefa kuri’a ta hanyar na’ura mai kwakwalwa ‘E-Boting’ musamman ganin abin da suka faru a lokacin da kungiyar ‘ICAN, da NBA suka yi amfani da tsarin.
“Jefa kuri’a ta hanyar na’ura mai kwakwalwa ba shi ne hanyar warware matsalar ba, musamman ganin yadda kowa ke yadda ya so tare da tsoron doka a kasar nan, lallai abin yana da mautuka wahala. A halin yanzu hukumar EFCC na bincikar abin da aka kira ‘E-Rigging’ a kungiyar NBA. Lamarin ‘E-Boting system’ zai matukar wahala saboda yawancin yan siyasan mu basu shirya ganin an gudanar da sahihin zabe ba a kasar nan,” inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!