Connect with us

LABARAI

ZABEN GWAMNA: Za Mu Hukunta Masu Cinikayyar Katin Zabe— Rundunar ‘Yan Sanda

Published

on

Rudunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama wasu mutane biyar da take zargi da sayen katin zabe a unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar kano da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar a jihar DSP Abdullahi Haruna Kyawa, shi ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce an kama mutanen ne bayan da suka samu labari.

‘Mutanen dai sun hada da mata, kuma ba a karamar hukumar Nassarawar kadai aka samu irin wadannan mutanen ba, har da karamar hukumar Dala’ inji jami’in.

Ya ce, da kyar suka kwaci mutanen daga hannun mutanen unguwannin da suka je sayen katin zaben.

DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce, dama tuni sun fuskanci cewa akwai wasu laifuka da mutane kan aikata a lokuta kamar kafin zabe da laifukan lokacin zabe da kuma na kafin a karasa zabe wato irin yanayin da Kanon ke ciki ke nan. Jami’in dan sandan ya ce ya kamata mutane su sani cewa ‘ Hukumar ‘yan sanda na sanar da su cewa saye da sayar da katin zabe babban laifi ne’. Ya ce laifin ba wai na masu sayen katin zaben ba ne kadai, har ma su kansu masu sayarwan suma ya shafe su.

DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce ‘ Zamu bi lungu da sako mu kamo duk wanda ya aikata irin wannan dabi’a, da wanda ya saya da ma wanda ya sayar dukkansu masu laifi ne, kuma za a yi bincike a kansu sannan a gurfanar da su a gaban shari’a’.

Jihar Kano dai ta shiga jerin gwanon jihohin da INEC ta bayyana cewa ba a kammala zaben ta ba, jihohin da suka hada da Adamawa da Binuwe da Sakkwato da Bauchi da kuma Filato.

Hukumar ta INEC ta sanar da cewa za a sake gudanar da zabukan a ranar 23 ga watan Maris, 2019 a jihohin da ta sanar da cewa ba a kammala zabensu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!