Connect with us

TATTAUNAWA

Bambancin PDPin Da,Da Ta Yanzu – Salim

Published

on

Zaben 2019 ta zo da wani irin sabon salon siyasa da ya baiwa matasa sababbin jinni damar shiga a dama da su sosai. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da dokar da gwamnati mai ci ta amince da ita ta cire dukkan shingayen da ke hana matasa tsayawa takara musamman a wasu manyan mukamai ba. Kan haka matasan sun yunkuro tare da tofa albarkacin bakinsu kan siyasar kakar zaben da ke dab da karewa. Wakilinmu, RABIÚ ALI INDABAWA ya yi kicibis da wani matashin dan siyasa, dan jamíyyar PDP, Salim Abdallah inda ya tattauna da shi kan yanayin siyasar ta zaben 2019, musamman ganin cewa a bangaren ýan adawa yake wanda ake ganin kamar bas u da ta cewa. Ku karanta hirar har karshe ku ji bayanansa.

Da fari za mu so ka fadawa masu karatu dalilinka na shiga tafiyar PDP
To Alhamdulillahi, dalilina na shiga wannan tafiya ta jam’iyyar PDP ba daya ba ne, amma babban muhimmi shi ne, wannan PDP ba irin waccan PDP din ba ce, domin a waccan ana ta samun rigingimu a wurare daban-daban, amma wannan a dinke take. Kuma kai din nan shaida ne babu wanda zai ce a yanzu muna da wata matsala da za ta tayar mana da hankali, wannan kai tsaye ya nuna nasara na tare da mu.

A na daf da fara zaben Shugaban Kasa, Gwamnatin APC kuma tana ayyuka a bayyane, wane kwarin gwiwa kake da shi kan samun nasara?
Ni har ka ba ni dariya, to ai kai ka ma fi ni sani

A a ni ban sani ba, tun da ni ai ba dan siyasa ba ne
To bari in gaya duk in da muka je muna samun nasara dari bisa dari, domin wannan hasashen shi yake nuna mana cewa mun ci zabe cikin yardar Ubangiji.

Shugaba Buhari ya karbi mulkin Kasar nan cikin wani kangi, yanzu kuma al’amura sun fara dai-daita, ba ka ganin barinsa kujerar a yanzu zai dawo da hannun agogo baya?
Da fari dalilin ma da ya sa shi Atiku Abubakar ya fito neman wannan kujera, don ya ceto ‘yan Nijeriya daga kangin wahalar da suke ciki, na talauci da sauran al’amura na rashin jin dadin rayuwa. Ka san shi mutum ne mai tausayin jama’a, ba ya so ya ga wani dan-Adam cikin kuncin rayuwa, bisa ga wannan tausayin ne ya ga ya dace ya zo ya ceto al’ummar Nijeriya, wannan shi ne makasudin fitowarsa takara.

Ina aka bar batun cewa da su aka yi watandar dukiyar al’ummar Nijeriya
Alhaji Atiku Abubakar ba barawo ba ne, kuma ai da kansa ya fito duniya ya yi shelar cewa duk wanda yake da shaidar cewa shi barawo ne, to ya fito shaidarsa mai karfi ya bayyana don a gurfanar da shi a kotu. Kuma baya ga haka, ni kaina ni Salim D. Abdallah na yada wannan a shafukana na Istagram, facebook, da kuma Tweeter, na kalu-balanci duk wani mutum da ya tabbatar min da cewa Atiku Abubakar ya yi sata har ya kawo min gamsassun hujjoji kwarara na sa masa kyautar naira dubu 300, kuma har yau har gobe ina nan a kan bakana ban janye ba.

Idan kai maganar Atiku zai yi aiki, sai na tuna har yanzu fa hanyar da za ka je Jihar Adamawa fa ba ta da kyau, an ya kuwa aiki zai yiwu a haka?
To ai wannan dalilin ne ya sa muke son mu samu wannan damar mu yi amfani da ita.

Malam Salim ina damar da ya samu ta Mataimakin Shugaban kasa shekara da shekaru, duk bai isa a yi aikin ba sai yanzu?
Ai ka san shi dan-Adam tara yake bai cika goma ba, wannan ajizanci ne na dan Adam, yanzu ya dawo don gyara kuskuren da ya yi a baya.

Ashe kun yarda an tafka kuskure kenan?
A’a an yi kuskure dai ba an tafka ba, kuma ai shi mutum ne, in ban da Annabawa waye ba ya kuskure? Ai dole ka same mu da kuskure a wani lokacin ma har da ganganci, amma dai duk da kuskure ai ko da babu Gwamnati a hannusa kowa ya san shi mai yi ne.

Arewa Maso Gabashin Kasa na fama da matsalar tsaro, ta yaya za ku magance wannan matsala idan kun ci zabe?
Kada fa ka manta Alhaji Atiku Abubakar tsohon Kwastam ne, ya san duk ta in da ake shigo da makamai da sauran kayan laifi domin ya kware a wurin. Bayan nan kuma ya yi mu’amala da mutane iri-iri da kungiyoyi daban-daban. Ai nib a ma na son a ke yin magana kan tsaro, domin ba da gaske a ke son a magance lamarin ba, da gaske ne da tuni abin da tuni ya zama tarihi.

Buhari fa tsohon Janar ne na soja, ba ka ganin ya fi Atiku sanin harkar tsaro?
A kwai wani abu da ba ka sani ba, idan mutum bai da niyyar yin abu a zuciyarsa na gyara ko shi menene ba zai iya kawo wannan gyara ba. Ai a zuciya yake, kamar ni da nake ba kowa ba, idan ina son magance abu a rayuwata in dai na niyya, to cikin kankanin lokaci zan magance shi. Saboda haka ba wai maganar tsohon soja ba ce magana ce ta zuciya, idan mutum yana da zuciyar taimako zai taimaka kawai. Don haka ne Alhaji Atiku Abubakar ya jajirce kan tsayawa kai-da-fata wajen ceto rayuwar talakawa. Ka da fa ka manta a lokacin da Boko Haram, a cikin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya taka rawa dari bisa dari, domin ba ma da ma’aikata ya hada kai ba, da ‘yan banga ya hada kai yanzu ga Adamawa nan zaune lafiya, kuma ta sanadiyyar Alhaji Atiku ne ba wai wani tsohon ba soja ba.

Uwar jam’iyyar PDP a baya ta koka cewa Mataimakin da Atiku ya tsayar bai tuntube su ba, ba ka ganin hakan zai iya kawo muku cikas?
Ka da ka manta don an tsayar da kai takarar Shugaban Kasa ba kai kake damar tsayar da mataimakinka ba, ai akwai na gaba da kai, jam’iyya gaba take da kowa ko da kana matsayin Shugaban Kasa jam’iyya ta fi ka sai dai idan ka ci zabe ka nemi shawarwari. Kuma ka san shi mutum ne mai daukar shawara ba mara daukar shawara ba.

Kenan karya ne ba a yi haka ba?
Kada ka manta shi fa ba mutum ne mai son nuna wariya ba, komai zai yi sai da shawara, don haka ba wai gaban kansa ya yi ba. Kuma ko a gidansa ma matansa in ka duba za ka ga WAZOBIA ne, akwai Bahaushiya, akwai Inyamura, akwai Bayerabiya, don haka a kan wannan tsari yake son ya dora Nijeriya Kasa daya al’umma daya, ka ji dalilinsa na dauko wannan mataimaki.

Zuwan da Atiku ya yi Amurka ana ganin kamar wata kullalliya ce da take da alaka da kalaman sayar da NNPC, me za ka ce kan haka?
Ka ji wani abin dariya, ai wannan maganganu ne na ‘yan APC ‘yan adawa suke yi, ta yadda za su bi su ga sun dakile kwarjini da farin jini na Atiku Abubakar, Atiku ya samu bizarsa ta shiga Amurka tun kafin ya yi wannan furucin, duk kannin mutum a duniya da za ka ji ya yi wani furuci yana da dalili. Saboda shi mutum ne jajirtacce da duk in da ya ji ana kawo matsala sai ya kawo gyara a wurin, baya shakkar mutum, ba ya tsoron ko waye kai, shi burinsa kawai ya ga ya tabbatar da gyara a Kasa, ko za a ji dadi ko ba za a ji dadi ba, duk wadannan zantuka ba za ka hana mutum fadar abin da zai fada ba. Sai ka ji mutum ya fadi wannan ya kamo wancan, amma ba shi da hujja sai dai kame-kame shi ne kawai, amma dai shi Atiku yana da kudiri mai kyau na son ya gyara Nijeriya

Buhari yana da abin fada a wurin kamfen saboda ayyuka da ya yi kuma bay a ba da ko sisi, ku da me kuka yi naku kamfen din?
To shi dai a yanzu Atiku Abubakar duk in da yake zagayawa wurin kamfen dinsa ba ya ba da ko kwandala, amma idan ka duba kamfen din Shugaba Buhari, ka je ka bincika ka ji nawa ake fitarwa daga aljihun Gwamnati? Ana fitar da makudan kudi ne domin a tara jama’a. ka duba zuwansa Kano, sai da aka je aka gayyato Gwamnoni guda uku daga Nijar.

Ashe ke nan hakan yana nuna kyakkyawar alakar Gwamnatin da makotan Kasar ko?
Ba wata alaka kawai dai wani salo ne na yin amfani da dukiyar talaka, su me yasa ba sa gayyatar na mu Gwamnnonin, kai dai a yi sha’ani kawai.

To a karshe wane kira za ka yi ga matasa, game da zaben da ake fuskanta?
Kirana ga matasa su fito su zabi wazirin Adamawa Alhaji Atiki Abubakar, sannan su kiyayi duk abin da zai kawo tashin hankali, Allah ya sa a yi zabe lafiya a gama lafiya.

Mun gode.
Ni ma nag ode.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!