Connect with us

WASANNI

Barcelona Ne Suka Rage Wakilan Sipaniya A Kofin Zakarun Turai

Published

on

Barcelona ta kai wasan daf da na kusa da na Karshe wato kwata fayinal, bayan da ta doke Kungiyar Kwallon Kafa ta Lyon 5-1 a karawar da suka yi a filin wasa na Camp Nou a ranar Larabar da ta gabata.
Barcelona ta ci Kwallayen ta hannu Lionel Messi wanda ya zura guda biyu a raga da wadda Coutinho da Pigue da kuma Dembele da kowannensu ya ci dai dai yayinda Ita kuwa Lyon wadda ta tashi wasan farko a Faransa 0-0, taci Kwallo ne ta hannun Lucas Tousart.
Kwallaye biyun da Messi ya ci ya sa yana da 108 a gasar cin kofin zakarun Turai, biye da Cristiano Ronaldo na Jubentus mai 124 jumulla kuma a karon farko Barcelona za ta wakilci Spaniya ita kadai tare da Kungiyoyi da suka hada da Jubentus da Manchester United da Manchester City da Liberpool da Tottenham da Porto da kuma Ajad.
Rabon da Kungiya daya ta rage a gasar zakarun Turai irin wannan matakin tun bayan shekarar 2010, a ranar Talata ne Jubentus ta fitar da Atletico Madrid a Italiya yayinda Real Madrid kuma tun satin daya gabata Ajad tayi waje da ita a gasar.
Rabon da a ce Kungiyoyin Spaniya sun kasa kai karawar daf da na kusa da na Karshe tun shekara ta 2005, sai dai kuma Barcelona ta hana hakan ya faru, bayan da ta kai bantenta a wasannin bana tunda har yanzu ba a fitar da ita daga gasar ba.
Sai dai mai koyar da ‘yan wasan Barcelona, Enesto Balberde, ya bayyana cewa zasu bawa marada kunya kuma za su kasance jakadun Kasar Sipaniya a gasar ta bana kuma yana fatan Kungiyarsa za ta lashe gasar ta bana duk da cewa akwai manyan Kungiyoyi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!