Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Amince Da Kashe Euro Miliyan 64.75 Kan Aikin Ruwan Kano

Published

on

A ranar Laraba ne, Majalisar zartarwa ta kasa, ta amince da kashe jimillan Yuro milyan 64.75 domin aikin inganta samar da ruwan sha a Jihar Kano.
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta bayyana hakan a lokacin da take yi wa manema labarai na fadar gwamnatin tarayya karin haske, bayan zaman da majalisar zartarwan ta yi wanda shugaba Buhari ya jagoranta a fadar ta shugaban kasa.
Ta ce, aikin wanda gwamnatin ta Jihar Kano ce za ta aiwatar da shi, zai inganta yanayin zaman al’umman na Jihar ta Kano.
“Aikin zai farfado da kuma samar da mahimman ayyukan da ake bukata da za su inganta samar da ruwan sha ga dimbin al’umman da ke Jihar ta Kano.
Ma’aikatar albarkatun ruwa a karkashin wani kwamiti da zai lura da aikin ne za su gudanar da aikin.
“Kudin aikin, gwamnatin tarayya ce za ta nemo su, sai gwamnatin ta tarayya ta rantawa gwamnatin ta Jihar ta Kano, a kan wasu saukakan sharudda.
Ministar ta ce, za a samo kudaden aikin ne daga wata kungiya ta kasar Faransa, a bisa ruwan kashi 1.02, wanda za a biya shi a cikin shekaru 20 a bisa biyan kashi-kashi na shakaru bakwai.
A cewar ta, akwai kuma kudin share fagen fara aiki da za a biya na kashi 0.25 na kudin.
Akalla Ministoci 28 ne suka halarci zaman majalisar ta zartarwa wanda shi ne na farko tun bayan kammala zabukan shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya da na gwamnoni gami da na ‘yan majalisun Jihohi.
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha, shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shugaban ma’aikata na tarayya, Winifred Oyo-Ita da mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Babagana Monguno, duk suna cikin wadanda suka halarci zaman majalisar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!