Connect with us

MANYAN LABARAI

El-Rufa’i Ya Karyata Jita-jitar Yin Hatsarinsa

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya karyata jita-jitar da ke cewa ya yi hatsari.
Wannan jitar-jitar ta yi ta yawo a kafafen yada labarai na zamani, inda aka ce ya yi hatsari, musamman a kafar sadarwa ta Facebook cewa wannan karya ce tsagoranta.
“Bayan na tashi daga bacci, sai na ji gari ya dauka cewa, wai na yi hatsari, wannan labari na kanzon kurege, na da dangantaka da irin labaran karyar da jam’iyyar PDP ke yada wa, har ma wai ana cewa, ina cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.
“Wannan labarin ba gaskiya ba ne. Masu yada wannan jita-jita sun kara min kwanaki. Saboda haka, da yardar Allah zan ci gaba da yaki da cin-hanci da rashawa, kuma Allah shi ne zai ci gaba kare ni, saboda haka masu son ganin bayana, ba za su iya ba, domin na san Allah na tare da ni, saboda haka, har za su gaji su daina.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!