Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Jigawa Ta Kashe Naira Biliyan 5.5 Wajen Biyan Tsofaffin Ma’iakata

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe Naira biliyan 5,546,638,643.59 wajen biyan ma’aikata hakkokinsu wadanda suka yi rataya da kuma sauran hakkokinsu daga watan Janairu zuwa Disambar na shekara ta 2018.
Babban Sakatare na jiha da kuma kananan hukumomin da ke jihar na Asusun ajiyar ‘yan fansho Hashim Ahmad Fagam ne ya sanar da hakan a hirar sa da manema labarai a kan ayyukan da suka yi.
Fagam ya ci gaba da cewa, daga cikin jimlar Naira biliyan 1,458,537,592.30 an biya wadanda suka yi ritayar su 889 na jiha da kuma na kananan hukumomin, inda kuma Naira biliyan 552,026,773.47 aka biya iyalan ma’aikatan da suka rasu a lokacin suna kan aiki.
A cewar Hashim Ahmad Fagam, kudin da aka biya na fansho daga watan Janairu zuwa Disambar na 2018, ya kai Naira 3,453,518,133.63, inda kuma Naira biliyan 79,260,679.14 an biya su ga iyalan ‘yan fanshon da suka rasu su 13 da kuma Naira 3,295,465.05 da aka biya wadanbda suka yi ritayar su 10 a matsayin kashi takawas bisa dari na abin da suke zuba wa a cikin asususn ajiyar na ‘yan fashon.
Ya ci gaba da cewar, zai iya fada ba tare da wata tantama ba, a yanzu gwamnatin jihar Jigawa babu wadi dan fasho da ke binta ko da kwabo daya.
Sakataren ya kuma bai wa ma’aikatan jihar tabbacin cewar, burin hukumar shi ne ta tabbatar da tan a kula da biyansu hakkokinsu a kan lokaci na yin rataya.
A karshe, ya kuma yaba wa gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar a kan hadin kan da yake bai wa hukumar da kuma goyon baya a kowane lokaci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!