Connect with us

LABARAI

Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Bayyana Ranar Rufe Karbar Kudin Kujera A Bauchi

Published

on

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi ta shaida cewar za ta rufe amsar kudin tafiya aikin hajjin bana (2019) ne zuwa ranar Juma’a 5 ga watan Afrilun wannan shekarar.
Babban sakataren hukumar jin dadin Alhazai ta jihad Bauchi, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa shine ya bayyana hakan lokacin da yake hira da ‘yan jaridu a ofishinsa da ke Bauchi. a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakin hukumar alhazai ta jihar Bauchi Muhammad Sani Yunusa ya aiko mana da ita ya shaida cewar hukumar tasu, tana kan gudanar da tsare-tsaren da suka dace domin kyautata aikin hajjin na wannan shekarar.
Hardawa ya kuma kara da cewa ranar 21 ga watan 2 da ta wuce ne ranar da hukumar alhazai ta kasa ta tsara kuma take sa ran kowani maniyyaci ya ajiye akalla rabin kudin aikin Hajji da aka biya bara wato kudin da bai gaza Naira 700,000 zuwa 750,000 don bada damar aika wa da bayanin maniyyacin zuwa shalkwaran Hukumar alhazai da ke Abuja, don daukan dukkan matakai da wuri na tabbatar da walwalansa yayin aikin hajji.
Babban sakataren ya yi kira ga al’ummar jihar Bauchi musamman maniyyata aikin hajji bana da su garzaya shalkwatan kananan hukumomin su ko ofishin hukumar Alhazai ke cikin Bauchi daura da shagon JIFATU dake cikin garin Bauchi don karbar takardar shigar da kudi a bankin domin samun nasarar samun kuje rar aikin hajji. Wannan shekarar.
Sanarwar ta nemi dukkanin masu niyyar tafiya aikin Hajji a wannan shekarar da su tabbatar da tuntubar hukumar domin samun bayanan da suka dace domin a samu nasarar kammala rijistar samun kujerar cikin hanzari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!