Connect with us

MANYAN LABARAI

INEC Ta Ba Zababbun ’Yan Majalisa Takardar Shaida

Published

on

A yanzun haka, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta tana mika takardun shaidar samun nasara ga ‘yan takaran da suka yi nasara a zaben da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, a duk sassan kasar nan.
Tun da farko, hukumar ta INEC ta bayar da sanarwar cewa wadanda sunayen su ya bayyana a shafinta na yanar gizo ne kadai za ta bai wa takardun shaidar.
A wajen bikin, shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, “Akwai ayyuka masu yawa a gaban hukumar ta INEC, alhalin kuma babu isasshen lokaci.
“Ina son na tabbatar maku cewa, za mu ci gaba da yin aiki tare da majalisun kasa wajen dubawa da karfafa dokokin zabe.

“Amma ina son na yi roko ga zababbun Sanatoci da su fara aikin tun da wuri, su kammala aiki a kan dokokin zaben a kan lokaci tun kafin babban zabe na 2023.
“Ina farin cikin ganin cewa daga cikin Sanatocin da aka zaba akwai wadanda muka yi aiki tare da su kud-da-kud.
Shugaban hukumar zaben yana sa ran ganin sun yi aiki tare da sabbin Sanatocin da aka zaba domin kyautata tsarin zabe na kasar nan.
Daga cikin Sanatocin da aka baiwa takardun shaidan: Sanata Ike Ekweremadu, Enugu ta yamma (PDP); Mohammed Sabo, Jigawa ta kudu maso yamma (APC); Philip Aduda, FCT (PDP) da Sanata Dino Malaiye Kogi ta yamma (PDP).
Sauran sun hada da; Baba Kaita, Kastina ta arewa (APC); Omo-Agege Obie Delta ta tsakiya (APC); Ibrahim Gandam, Yobe ta arewa (APC); Abdul’Aziz Yari, Zamfara ta arewa (APC); Kaura Yahaya, Zamfara ta yamma (APC) da Ifeanyi Uba, Anambra ta kudu (YPP)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!