Connect with us

MANYAN LABARAI

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro Kan Zabukan Da Aka Yi

Published

on

Jam’iyyun adawa a jihar Bauchi da ‘yan takararsu na gwamna sun kira taron manema labarai a ofishinsu da ke kan hanyar Maiduguri a jiya Alhamis, inda suka bayyana matsayarsu na amincewa da shirin sake gudanar da zaben gwamna a wasu mazabu na kananan hukumomi 14 da kuma karamar hukumar Tafawa Balewa baki dayanta.
Alhaji Abubakar said sardauna dan takarar gwamna kuma shugaban jam’iyyar PPN shi ne ya fara jawabi inda ya ja hankalin jama’a da su ba hukumar zabe goyon baya kan kudirinta na sake zabe a wuraren da ake ganin zaben na ranar Asabar bai kammala ba.
Don haka ya ce a matsayinsu na ‘yan takara kuma magoya bayan jam’iyyu suna son INEC ta sa adalci cikin duk abin da aka shirya game da sake zaben.
Mohammed Garba Bature Ningi shugaban jamiyyar NEPP Wanda ya zo daga karamar hukumar Ningi cikin jawabinsa ya ja hankalin jama’a da wannan lamarin ya Shafa kowa ya fito a yi zabe lafiya a nisanci tashin hankali. A sani ko su ‘yan siyasa suka samu matsala hukumar zabe ke warware musu matsalar, don haka ya ce suna bin doka da goyon bayan sake zabe a yankunan da aka ayyana.
Hamisu Isa shugaban jam’iyyar ACPN a jihar Bauchi shi ma ya bayyana kudirinsa na goyon bayan hukumar zabe kan sake zabe a yankunan da ta bayyana.
Shi ma Kwamared Abdullahi B. Mohammed shugaban jam’iyyar APN Wanda ya jagoranci zaman ya ja hankalin hukumar zabe ta kasa kan su rika bin doka wajen jin koken kowa da kowa. Ya ce, suna goyon bayan hukumar zabe kan gudanar da zaben amma ba su ji dadin yadda ake daukar koken wasu ake kin daukar na wasu ba.
Don haka ya yaba game da kwamitin da aka nado daga Abuja amma ya ce suna jira su ji abin da kwamitin zai ce yayin zama da masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasa. Saboda sun fahimci kwamitin ba shi da wani hurumi a shari’a kan aikin da zai gudanar.
Jam’iyyun masu dan takarar gwamna da suka shiga cikin wannan zaman guda 21ne, sannan kuma akwai uku marasa ‘yan takara wato, ADC da PDC da DA da MPN da DPC da NEPP da MMN da SDP da Kowa da ACPN da PPN da BNPP da APP da NRM da UPN da SNP da APA da AA da AGA da HOPE cikin su guda uku ba su da ‘yan takarar gwamna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!