Connect with us

LABARAI

Jinkirta Bayyana Sakamakon Barazana Ce Ga Zaman Lafiya A Bauchi — MYF

Published

on

Wata kungiya mai suna ‘Bauchi Metropolitan Youth Forum’ ta shaida cewar akwai gayar matsala da ci gaba da jinkirta bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, kungiyar tana mai shaida cewar a bisa ababen da suke faru yanzu haka a cikin jihar, kamatuwa ya yi hukumar zabe ta baiwa jama’an jihar abin da suka zaba cikin ruwan sanyi domin gudun tashin hankali da fitina da hakan ka iya kawo rudani a cikin jihar.
Kungiyar ta yi wannan bukatar ga INEC ne a jiya, sa’ilin da suke gabatar da taron manema labaru a NUJ da ke Bauchi. Shugaban kungiyar Umar A. Aliyu shine ya jagoranci zaman, yana mai shaida cewar yanzu haka matasa a jihar sun fara fusata da wannan jinkirin, yana mai neman hukumar zabe INEC da ta duba zaman lafiya da ci gaban jihar ta kauce wa dukkanin yunkurin biye wa hanyoyin da za su kawo tashin hankali a jihar, don haka ne ya nemi INEC ta ayyana wanda ya samu nasarar yanzu.
Umar Aliyu yake cewa; “Abubuwan da suke kokarin faruwa mu al’umman jihar Bauchi ba mu goyon bayansu kuma ba za mu goyi bayansu. INEC ta tabbatar da cewar zaben da aka yi a Bauchi bai gama kammaluwa ba, wanda mu a saninmu da kuma bayanan da muka samu daga cikin kalaman da baturiyar zabe daga Tafawa Balewa ta bayar, ta ce an yi zabe cikin kwanciyar hankali da laluma. Wanda ta bayar da dalilai a wajen da take gabatar da sakamakon zabenta, to amma sai wasu ababen da suka faru wadanda ta bayyana da basu kai a ce an soke zaben nan ba da su aka fake. Mu ba mu goyon bayan hakan,”
Ya ce, zaman lafiyar jihar suka fi so a kan komai,
domin a cewarsu ba su da wani wajen zuwa da ya wuce jihar ta Bauchi, “ba mu da wata jihar da ta wuce Bauchi, idan yau aka ce mu bar Bauchi babu inda za mu je. Matsaloli sun fara faruwa a cikin garin Bauchi a bisa kin bayyana wanda ya samu nasarar cin zaben gwamnan jihar Bauchi, wasu unguwanni kamar su Doya, da Filin Idi zuwa ta Bakaro an samu rahotonnin tashin hankali a cikinsu, to mu zaman lafiyar jihar muke so da zaman lafiyar jama’an jihar.
“Muna rokon gwamnatin tarayya muna kuma rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sani mu muna mutane ne da muke sonsa kuma mun yi masa amana, muma yanzu muna neman agajinsa ya shigo cikin lamarinmu.
“Sannan muna kuma kira ga hukumar INEC ta kasa ta sani ido na kanta, muna neman a bayyana wanda ya ci nasara domin kwanciyar hankalin jama’anmu, yanzu haka jama’a sun fara tayar da harzitsi don haka muna shaida wa duniya cewar bayyana wa jama’a wanda suka zaba kawai shine zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiyan jihar,” Inji shi.
Ya bayyana cewar zaman lafiyar wadanda suka fadi shine su amshi kayan da suka sha kawai domin komai ya tafi bisa tsari, yana mai neman masu ruwa da tsaki kan lamarin da su shigo cikin lamarin domin bayyana Sanata Bala Muhammad a matsayin sabon gwamnan jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!