Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Dakatar Da Sake Zaben Gwamna A Wasu Rumfunan Jihar Adamawa

Published

on

A ranar Alhamis ne, Babbar kotun da ke Yola, ta bayar da umurnin hana hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta sake zaben gwamna a wasu rumfunan zabe na Jihar Adamawa.
A sakamakon yanda hukumar zaben ta shelanta zaben wasu Jihohi da wanda bai kammala ba, da suka hada da Jihar ta Adamawa, hukumar ta INEC ta sanya ranar 23 ga watan Marisn a matsayin ranar da za a sake zaben.
Alkalin babbar kotun jihar, Abdulaziz Waziri ya bayar da wannan umurnin ne sakamakon karar da Jam’iyyar MRPD ta shigar na neman hakan.
Kaungiyar ta yi zargin cewa, an tsame tambarinta daga takardar kada kuri’a a zaben da aka yin a ranar 9 ga watan na Maris a Jihar.
A ranar Laraba, Jam’iyyar PDP, ta yi gargadi tana mai zargin gwamnan Jihar, Jibrilla Bindow, da shirin yin amfani da jam’iyyar ta MRPD, wajen watsa zaben na baya a da aka shirya gudanarwa.
“Suna nufin yin amfani da wani dan takara wanda yake zargin cewa wai babu tambarin jam’iyyarsa a takardun da aka yi zaben na gwamna da su, ya ma shigar da kara kan hakan a gaban kotu.
Da yake mayar da martani a kan hakan, babban jami’in zabe na Jihar, Kashim Gaidam, cewa ya yi babu wani umurni daga kotu da ya yi umurnin a dakatar da zaben.
“Yana mai cewa, shalkwatar hukumar zaben ne kadai take da bakin magana a kan duk wata kara da aka shigar a gaban kotu,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!