Connect with us

LABARAI

Kujerar Gwamna: Dattawan APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zabe A Karamar Hukumar Bauchi

Published

on

Dattawan jam’iyyar APC da kuma wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar Bauchi karkashin kungiyar ‘Concerned Elders of the APC and Senior Citizens of Bauchi,’ sun yi watsi hadi da fatali da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a cikin karamar hukumar Bauchi, suna masu neman INEC ta sake gudanar da sabon zabe a karamar hukumar.
Shugaban kungiyar Alhaji Yarima Aliyu Giade (Ajiyan Giade) shi ne ya yi wannan bayanin a wani taron manema labaru da suka kira a jiya a Bauchi, yana mai shaida cewar allura ne ta tona garma, inda yake mai shaida cewar suna kallon hukumar zabe INEC a matsayin wacce take kwangaba-kwan-baya a cikin harkokinta.
A cewar kungiyar; “INEC ta ce za a sake gudanar da zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, kuma yanzu sun dawo wai sun kafa kwamiti domin ya yi nazarin da bincike, wannan zamu dauka, tun da INEC ta rigaya ta yanke hukuncin za a sake gudanar da zaben nan kamatuwa ya yi a tsaya a haka.“Muna son mu sanar da jama’a da kuma duniya baki daya, tun da dai hukumar zabe mai zaman kanta INEC tana yin amai ta lashe ko kuma, in ta fadi abu ta sake dawowa a kai, an yi maganar cewar zaben Tafawa Balewa ba a kammala shi ba, yanzu kuma an turo kwamiti ya zo ya sake duba wannan maganar da aka yi.
To, tun da ana magana a tafi gaba a dawo baya, muna son mu fada wa INEC zaben da aka yi a karamar hukumar Bauchi ta gwamnan jihar ba mu amince da sakamakon zaben ba, zaben kuma bai yi ba, ba mu yarda da zaben ba, muna bukatar a soke zaben domin tabbatar da adalci,” Inji kungiyar Dattawan.
Sun bayyana cewar dalilansu na neman a soke zaben sun hada da aringizon kuri’u da barazanar da aka yi wa mutanensu, don haka ne suka nemi a sake gudanar da zaben.
Meye sa baku kawo zancen ba sai da aka turo kwamitin nan? “Abun da ya sa sai yanzu muka kawo wannan batun, a matsayinmu na masu bin doka, duk abun da aka ce INEC ta fada doka kuma ta fada shi kenan ya mana. Amma idan aka fadi magana aka tafi aka je kuma aka sake dawowa, babu dalilin da zai sanya INEC ta ce ta soke zaben Tafawa Balewa kuma a zo a kafa wani kwamiti domin duba wannan zancen ka ga wannan yana iya kawo rudani,” Inji shi.
Kwamitin dattawan ta kara da cewa, “Tun da an ce za a duba batun Tafawa Balewa to muna son a duba batunmu tun da mun ki amincewa da sakamakon zaben karamar hukumar Bauchi,” A cewar Dattawan.
A gefe guda kuma Dattawan APC din, sun nemi jama’an da sake zaben kujerar gwamna a turmi na biyu ya shafa da su fito kansu da kwarkwatarsu domin sake jefa kuri’arsu domin zaben wanda suke so.
Kungiyar ta kuma yi suka mai karfi ga Kakakin majalisar tarayya a bisa zarginsa da yayi wa gwamnan jihar Bauchi na daukan nauyin ‘yan sara-suka a lokacin gudanar da zaben a can yankin Tafawa Balewa, kungiyar ta ce zargin na Dogara bai da tushe balle makama.
Wani binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewar yanzu haka dai kwamitin da INEC ta turo daga Abuja domin bincike kan matsalar da aka samu a karamar hukumar Tafawa Balewa sun shigo cikin jihar hadi da fara gudanar da bincikensu domin tattaro hakikanan abun da ke akwai, inda ake
tunanin za su iya amincewa da zaben da aka yin ko kuma su tabbatar da sake gudanar da zaben.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!