Connect with us

LABARAI

Kungiyar Gwadago Ta Bukaci Shettima Ya Biya ‘Yan Fansho Naira Biliyan 20 Kafin Ya Bar Ofis

Published

on

Gamayyar kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), reshen jihar Borno, ta bukaci gwamnan jihar Borno -mai barin gado, Alhaji Kashim Shettima, da cewa ya biya yan fanshon jihar bashin naira biliyan 20 wadanda tsuffin ma’aikatab ke bin sa bashi, kafin ya bar kujerar gwamnan jihar.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar NLC da ke jihar Borno, Mista Titus Abana, a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai, na Nijeriya (NAN), a birnin Maiduguri.
Abana ya bayyana cewa, marabin gwamnatin jihar da ta biya tsuffin ma’aikatan hakkokin su, na garatuti shi ne wanda aka biya a shekarar 2013, yanayin da ya jefa jama’a cikin halin ni’yasu.
“Duk da kuma kudin da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi na ‘Paris Club Refund’, amma gwamnatin jihar Borno ta ki ta biya yan fanshon hakkokin da suke bin gwamnati bashin”. Inji shi.
“Saboda haka ne muke kira ga gwamna a kan ya yi kokarin sauke nauyin hakkokin bashin tsuffin ma’aikatan, kamar yadda ya yi alkawari, kafin ya bar ofis”.
“saboda yadda ya sha ikirarin ba ya son bar wa magajin sa basussuka, tare da alkawarin biyan hakkokin ma’aikatan; fansho da ariyas, wadanda suka tattaru a wuyan gwamnatin sa da wadda ta gabace shi”.
“Kuma muna kara tuna masa kan cewa ya biya basukan kudin karin girma da na hutun ma’aikatan, wadanda suke a kan wuyan sa- yau kimanin shekaru uku da suka wuce, bayan kammala aikin kwamitin tantance ma’aikatan”. Ya nanata.
“Wanda har yanzu babu wani ma’aikacin da ya ci gajiyar wannan karin girman, tun bayan shekara ukun da suka gabata, bayan aikin tantance su”. Ya nanata.
Mista Abana ya koka dangane da halin da ma’aikatan suka shiga na yanayin matsi tare da matsalolin rayuwa kala- kala. Inda ya kada baki ya ce, “wanda da dama daga cikin yan fanshon suka mace ta dalilin matsin rayuwar”.
Bugu da kari kuma, shugaban kungiyar kwadagon, ya bukaci gwamnan da cewa yi hobbasa wajen raba wa ma’aikatan jihar rukunin gudajen gwamnati 1, 000, wanda hakan zai taimaka wajen rage karancin gidaje.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!