Connect with us

RAHOTANNI

Likitoci Musulmai Za su Gina Asibiti A Kaduna

Published

on

Kwararrun likitoci Musulmi ta kasa reshen jihar Kaduna IMAN, ta bayyana cewa, za ta gina asibitin da zai dinga kula da matsalolin rashin lafiyar ‘yan uwa Musulmi da kuma sauran al’ummar da ke cikin jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar Abubakar Isa-Balarbe ne ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron laccar da reshen kungiyar da ke a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ya shirya a Shika Zariya, da ke a jihar Kaduna.
Taken taron na bana dai shi ne: “Yadda ake amfani da siyasa da kungiyoyi a fannin kiwon lafiya a Nijeriya”.
Taron na daya daga cikin ayyukan da kungiyar ta gudanar na shekara, karo na biyar da kuma ayyukan tallafa wa marasa lafiya na mako daya na 2019.
Shugaban ya ci gaba da cewa, kungiyar ta yi tunanin gina asibitin ne gannin yadda ake da bukatar taimaka wa kiwon lafiya musamman ga talakawa.
A cewarsa, yunkurin abu ne da ya zo a kan gaba don yin aikin na samar da lafiya ga Musulmi kyauta. Ya kara da cewa, kungiyar ta yi aikin ga wadada suka amfana har su kimanin 140 a cikin 2019. Ya ce, bisa cim ma wadannan nasarorin, suna son su gina asibi da yardar Allah nasu na kansu don amfanin marasa karfi da ke cikin jihar Kaduna.
A cewar Isa-Balarbe idan aka gina asibitin, zai gudanar da ayyukansa kyauta, nusamman don rage wa takawa kashe kudi wajen neman lafiyarsu.
Saboda haka sai ya yi kira ga masu hannu da shuni musamman Musulmai su bayar da gudummowarsu wajen ganin an cim ma nasarar da aka sa a gaba. Sannan kuma sai ya yi nuni da cewa, Manzon Allah SAW ya yi mana hudubar mu kaunaci ‘yan uwanmu, inda ya ce, wasunmu suna fita kasashen waje ne don neman lafiyarsu saboda ba za a iya yi musu magani a kasar nan ba. Ya ce shin me ya sa masu fita wajen ba za su zuba kudin nasu a yi musu aikin a kasar nan ba yadda hakan zai zama ‘sadakatijjariya’ takawa su amfana.
Ya ce miliyoyin Naira da Musulmi suke kashewa wajen sayen motocin alfarma da gina manyan gidaje masu tsada kamata ya yi su yi amfani da kudaden wajen daukaka addin Allah da taimaka wa lafiyar marasa karfi.
Isa-Balarabe ya ce akwai kuma bukatar mayar da hankali wajen ciyar da ilimin zamani gaba da samar da sana’oin dogaro da kai musamman ga matasa, inda ya yi nuni da cewar irin wannan aikin kamar ‘sadakatijjariya ce.
A cewarsa, a zamanmu na masu kiwon lafiya akwai yarjejeniyar da muka kulla da Allah na yi wa al’umma aiki. Isa-Balarabe ya yi nuni da cewar, rayuwar al’umma ta ki yin daidai ce saboda ba sa bin umarnin Allah. Ya kuma yaba wa reshen na asibin koyarwar da ke Shika a kan yunkurin su na son gina asibitin tare da yin kira ga sauran rassan kungiyar da ke fadin kasar nan su yi koyi da su a kan hakan.
A Taron kungiyar ta yi gwaje-gwaje da kuma yin tiyata kyauta ga marasa lafiyar har su 140 da kuma duba wasu marasa lafiya su 2,500. Sauran ayyukansa kan da kungiyar ta yi sun hada da, duba lafiyar almajirai su 300, ba su abinci, raba masu rigunan sanyi a Hayin Katsinawa, Shika cikin karamar hukumar Giwa da ke Kaduna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!