Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Si Yi Dan Wasan Tottenham Da Araha

Published

on

Rahotanni daga Kasar Belgium sun bayyana cewa Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United zata siyi dan wasan baya na Tottenham ta Kasar Ingila akan kudi fam miliyan 26 sabanin fam miliyan 60 da Tottenham din ta buKata tun farko.
A kakar wasan data gabata ne dai Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United taso siyan dan wasa Toby Alderweireld sai dai Tottenham ta dage cewa dole sai United din ta biya fam miliyan 60 kafin ta siyar mata da dan wasan dan asalin Kasar Belgium.
Sai dai har yanzu dan wasan bai sake sabuwar yarjejeniya da Kungiyar tasa ba wanda kuma hakan yake nufin a kakar wasa mai zuwa farashin dan wasan zai dawo fam miliyan 26 ga duk Kungiyar da take son siyansa.
Tsohon kociyan Kungiyar manchester United, Jose Mourinho ne dai yayi zawarcin dan wasan sai dai Kungiyar ta United a wancan lokaci bata bashi goyon bayan kashe maKudan kudade ba akan dan wasan da shekarunsa suka kusan zuwa 30.
Sai dai duk da cewa kawo yanzu ba Manchester United kawai take zawarcin dan wasan amma kuma itace akan gaban Barcelona wajen neman dan wasan wanda yakoma Tottenham daga Kungiyar Ajad ta Kasar Holland.
Har ila yau dan wasa Paul Pogba yana shirin sake sabuwar yarjejeniya da Kungiyar ta United wanda babban labarine ga magoya bayan Kungiyar wadanda sukaji tsoron tafiyar dan wasan a lokacin da Mourinho yake zaune a Kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!