Connect with us

RA'AYINMU

Matsalar Watsi Da Gine-ginen Da Ba A Kammala Ba

Published

on

Watsi da gine-ginen da ba a kammala ba, ya zama ruwan-dare a Jihohin wannan kasa da ma Birnin Tarayya, Abuja. Ko shakka babu, wannan wata gazawa ce ko abin kaico ga wannan kasa tamu baki daya. A wani bincike na kwana-kwanan nan, ya bayyana kimanin sama da gine-gine 665 da aka gaza kammalawa a Abuja, da ya hada da gidajen zama da kuma na kasuwanci. Abu ne mai sauki ka ga an yi watsi da katafaren gida na Milyoyin kudi a Abuja.
Haka nan, baya ga rashin kyan gani da wadannan gine-gine da aka yi watsi da su ke da shi, yana kuma zama barazana musamman ta bangaren tsaro ga wadanda ke makwabtaka da su, ta hanyar zama wata mafaka ta masu aikata laifuka ko ‘yan ta’adda da ke labewa suna cin karensu babu babbaka a ci. Koda yake, wasu na ganin cewa matsalar watsi da gine-ginen da ba a kammala ba, ko dai rashin tsari ne na masu mallakin wurin ko kuma kawai rashin ko-in-kula ne irin na masu hannu da shuni, musamman wadanda suka wawashi dukiyar al’umma da ba za su iya kaiwa banki ko gida su boye ba. Saboda haka, ko ma dai mene ne, wannan ya saba da tsarin da gwamnati ta tanadar akan harkar da ta shafi gidajen zama da na kasuwanci don amfanin al’ummarta.
Wadannan gidaje na nan da dama a cikin birane da wajensu da aka yi watsi da su. Wasu almajirai da nakasassu ne ke kwana a ciki, wasu kuma masu karamin karfi wadanda ba za su iya kama haya ba ne suka samu suka makale a ciki, ganin cewa babu wani wanda zai zo ya daga musu hankali ko ya bigi kirji ya ce da su nasa ne. A wasu lokutan, irin wadannan gine-gine kan rushe har su yi sanadiyyar rasa rayukan wasu da ba su ji ba, ba su gani ba. Haka kuma, wasu daga cikin irin wadannan gine-gine da aka yi watsi da su, gwamnati ce da kanta ta kwace daga hannun wasu ta kuma musanya musu da wasu amma ta yi watsi da su.
Har ila yau, daukar tsawon lokaci ana Shari’a Kotu a kan matsalar ire-iren wadannan gidaje, shi ma na taimakawa wajen matsalar watsi da irin wadannan gine-gine, yana kuma kawo tsaiko wajen kammala su. Bugu da kari, abin haushi da takaici, bincike ya nuna mafiya yawan wadannan gine-gine da ba a kammala ba, mallakar gwamnati. Amma saboda yanayi na cin hanci da rashawa da ke kewaye da gwamnatoci, yasa kacokan ba ma a tunawa da su ko ba su muhimmanci ballantana a kai ga kammala su, an fi so a bar su kullum kudinsu na sake hauhawa. Don haka, a nan wannan gidan Jarida bai ware kowa ba, daga kan gwamnati zuwa sauran daidaikun mutane da suka mallaki wadannan gidaje, ya zama wajibi Hukumar wannan kasa ta yi doka ta magance matsalolin watsi da irin wadannan gine-gine da aka yi watsi da su.

Kazalika, a baiwa wadanda ke da kwarewa a wannan bangare na gine-gine dama da sauran duk wani abu day a kamata don kammala wadannan gidaje ta yadda a nan gaba ba za a samu matsala ba. Don kuwa wannan hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati na kawar da ire-iren wadannan gidaje da ba a kammala ba, da ka iya zama barazana ga tsaro ko lafiyar al’ummar wannan kasa baki daya. Idan muka yi la’akari da wasu daga cikin kasashen Afrika da dama, irin wadannan gine-gine da aka yi watsi da su ba su da yawa, ‘yan kadan ne idan muka kwatanta da na wannan kasa. Dalili kuwa, akwai haraji da ake sanya gidaje ko ana amfani da su ko ba a kammala gininsu ba, babu daga kafa wajibi ne sai kowa ya biya musu haraji kamar yadda doka ta tanada.
Yana da matukar muhimmanci a fara amfani da irin wadannan dokoki a Nijeriya, dalili kuwa wannan zai baiwa duk wani wanda ke da irin wadannan gidaje azamar kammalawa saboda ya san dole ne sai ya biya musu haraji. Sannan ita kanta gwamnati ya zama wajibi ta mayar da hankali wajen kammala wadannan gine-gine nata da ta yi watsi da su, don ko babu komai za ta rika samun kudin shiga ta hanyarsu. Babban abin mamaki da tsoro shi ne, me yasa irin wadannan gidaje na Milyoyin kudi ake yin watsi da su? Lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi kasar nan, ya yi barazanar karbe irin wadannan gidaje ya mika su a hannun Jami’an tsaro don yin amfani da su a matsayin Shalkwatarsu ko kuma baiwa ma’aikata su shiga cikin su zauna kyauta. Ko shakka babu, yin hakan kan iya zama babbar maslaha ta magance matsalar, amma hakan bai yiwu ba saboda mafiya yawan masu wadannan gidaje ‘yan Siyasa ne da ke kewaye da gwamnatin ta kowane bangare.
A karshe, muna sake yin kira ga gwamnati, ta dubi bukatar rage ko magance matsalar yawaitar wadannan gine-gine da aka yi watsi da su a duk fadin wannan kasa, wadanda kai tsaye ke kawo mummunan barazana ga harkar tsaro da kuma asarar dimbin rayuka a lokacin da ya tashi rushewa, sannan Uwa-Uba ya zama wata matattarar ‘yan ta’adda da ke watayawarsu a ciki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!