Connect with us

MANYAN LABARAI

Mun Amince Da Kayen Da Muka Sha, A Ba Wanda Ya Ci Zaben Gwamnan Bauchi –Dan Takarar ACPN

Published

on

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar ACPN, Injiniya Abubakar Abbas, ya shaida cewar sun amince da kayen da suka sha bayan gudanar da zaben gwamnan jihar, yana mai bayanin cewar zaben ya gudana bisa gaskiya da adalci don haka ne suke kiran a baiwa wanda ya samu nasarar ci cikakken damarsa ta zama sabon gwamnan jihar.
Injiniyan ya shaida cewar yin hakan shine zai tabbatar da demokradiyya a tsakanin jama’a, yana mai bayanin a jiya lokacin da suka hallara a ofishin ‘yan jaridu da ke Bauchi, da yake samun rakiyar shugabanin kungiyar ‘yan kasuwa a jihar, sun nemi INEC ta tabbatar da nasarar wanda ya cin domin daurewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Injiniya ya nuna rashin kwarin guiwar su ga hukumar zabe INEC a bisa wasa da hankalin jama’an jihar da take yi na kin sanar da wanda ya lashe kujerar, kana ya nuna damuwarsa kan aikace-aikacen da jami’an ‘yan sanda ke yi wajen musguna wa jama’an jihar, “Ina matsayin dan takarar gwamna amma wani jami’an ‘yan sanda mai suna Baba Yola yake neman musguna min, don haka muna kira ga jami’an tsaro da suke gudanar da aiyukansu su daina shiga hidimar siyasa,” Inji shi.
Ya ce, “Dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad Abdulkadir shine ya ci nasarar zama gwamnan jihar Bauchi da dukkanin matakan zama gwamna domin jama’an jihar sun zabe shi, an kuma gudanar da zaben nan bisa gaskiya da adalci, don haka ina kira ga INEC ta tabbatar masa da kujerarsa domin komai ya tafi daidai,” in ji shi.
Harisu Mai Goro shi ne mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Bauchi ya nuna gayar damuwar su kan yadda matasa suka fara fusata da rashin bayyana sakamakon, yana mai cewa akwai barazana da hakan ke jawo wa ci gaban jihar don Haka ne ya nemi INEC ta bayyana Wanda ya lashe kujerar domin damin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya ce, “Idan matasan nan suka tayar da hankali domin zai shafi tattalin arziki da ‘yan kasuwarmu, don haka muna kira ga INEC ta sanar da sakamakon zaben nan domin gudun tashin hankali a fadin jihar ta Bauchi,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!