Connect with us

LABARAI

NDA Ta Kara Bukatar Neman Shiga Makarantar Na Mako biyu

Published

on

A jiya Alhamis ne wa’adin Makarantar koyar da manyan hafsoshin soja ta Nijeriya (NDA) domin amincewa da shiga makarantar domin horaswa karo na 71 ya cika, sai dai bayan cikar wannan wa’adi hukumar makarantar ta amince da kara mako biyu nan gaba, domin a sake ba masu bukata dama.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na makarantar Manjo Abubakar Abdullahi, wanda ya ce, an kara wa’adin zuwa ranar Alhamis 28 ga Maris, 2018. Saboda ya ce, wannan babbar dama ce ga wadanda ba su samu sun mika bukatun nasu ba a baya, don haka sai ya buka ce su da su gaggauta yin hakan kafin wa’adin na karshe ya cika.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!