Connect with us

RAHOTANNI

Rashin Kula Da Iyakokinmu Ke Sa Miyagu Shigo Wa Nijeriya –Mista Brigitte

Published

on

Majalisar dinkin Duniya za su taimaka wa Nijeriya wurin rage kwararowar bakin haure.
Jakadun Nijeriyan dai sun kara wata ganawa ta biyu ne da wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu kula da ‘yan gudun hijira don magance wannan matsala ta bakin haure.
Da take magana wakiliyar Majalisar Dinkin Duniyar kuma mataimakiyar shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke bangaren hukumar kungiyar kawancen Afirka Misis Brigitte
Mukanga-Eno ta ce; ya zama wajibi hukumomi da masu fada adji na Nijeriya su mike tsaye wajen kula wa da iyakokin kasashen da suka hada da Nijeriya, saboda barin mutane kowane iri na shigo wa yakan janyo bata-gari na samun damar shiga kasar suna aikata ayyukan ta’addanci.
Ta ce; Majalisar Dinkin Duniya za ta taimaka wa Nijeriya wajen dakile shigowar bakin haure masu shigo wa da sunan ‘yan gudun hijira.
Ta ce; akasarin bata-gari suna daukar wanan hanyar ce ta zama ma fi sauki su shigo kasashe suna ta’addanci. Ta kara da cewa tun a watan Nawambar bara Majalisar Dinkin Duniya ta
bukaci gwamnatin Nijeriya da ta tabbatar hukumar kula da kan iyakokin
kasarta sun sa ido sosai a kan Bodojin da ke Jihohin da suke da iyaka da wasu kasashe.

Ita ma a nata jawabin Babban hadimar gwamnatin Nijeriya da ke kula da sansanonin gudun hijira Malama Sadiya Faruk ta ce; wanan shawarar abin dubawa ce kuma abin a yi amfani da ita ce.
Saboda a wasu lokutan mutane na tururuwa zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira ba tare da an san daga ina suke ba .
Amma suna amfani da sunan ‘yan gudun hijira har ma wasu lokutan ka ga an tarar da abubuwan cutar da al’umma a sansanin ko kuma a kai hare-haren ta’addanci a sansanin. Ta ce; yana da gayar mahimmanci ga Nijeriya a matsayinta ta na Babban kasa ta yi amfani da Bodojinta wajen kariya ga al’ummar kasarta.
Taron na masu ruwa da tsaki ya maida hankali kan yadda ita ma kungiyar Tarayyar Afirika za ta yi am fani da jami’an tsaronta na kan iyakokin kasa da kasa wajen dakile ire-iren wadanan mutane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!