Connect with us

WASANNI

Real Madrid Suna Neman Bellarin Na Arsenal

Published

on

Rahotanni daga Kasar Sipaniya sun bayyana cewa nan gaba kadan ne Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid dake Kasar Sipaniya za ta nemi dan wasan baya na Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal, Hector Bellerin a lokacin bazara.
Kungiyar da ke mataki na uku akan teburin laliga ta fara bibiyar dan wasan dan asalin Kasar Spaniyan mai shekara 22 ne tun shekarar 2014 lokacin yana matashin dan wasa kuma har yanzu suna bibiyar Kwallonsa.
Bellerin, ya koma Arsenal ne daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona a shekarun baya bayan da ya haska a Karamar Kungiyar ta Barcelona sai dai kawo yanzu dan wasan yana jiyya inda zaiyi zaman watanni tara baya wasa sakamakon rauni dayaji a Kafarsa ta dama.
Kungiyar Kwallon Kafar ta Barcelona itama tana zawarcin tsohon dan wasan nata wanda take ganin yanzu girmansa ya kai yakoma Kungiyar domin cigaba da buga wasanni kuma a shirye take data sake nemansa.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Jubentus ma a kwanakin baya ta taba nuna sha’warta akan dan wasan sai dai tun a lokacin Arsenal tace dan wasan nata bana siyarwa bane wanda hakan yasa Jubentus taja baya.
Mai koyar da ‘yan wasan Kungiyar ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa dan wasan nasa baya daga cikin ‘yan wasan da zasu iya barin Kungiyar nan kusa inda yace dan wasa ne wanda zai dade yana buga wasa a Kungiyar ta Arsenal.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!