Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Shiga Zawarcin Milenkobic-Sabic

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta shiga zawarcin dan wasan tsakiyar Kungiyar Kwallon Kafa ta ta Lazio, Sergej Milenkobic-Sabic domin Kara Karfin ‘yan wasanta na tsakiya kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Milinkobic Sabic ya zura Kwallaye 14 cikin wasannin daya bugawa Kungiyar wanda hakan yasa Kungiyoyi da dama irinsu Barcelona da Manchester United suka shiga zawarcin dan wasan mai shekara 24 a duniya.
Dan wasan baiyi KoKari ba a gasar cin kofin duniyar daya wakilci Kasarsa ta Serbia kuma kawo yanzu a wannan kakar Kwallo uku kacal ya zurawa Kungiyar taza ta Lazio a raga sai dai kuma yana buga wasa a kowanne lokaci.
Amma kuma Barcelona da Manchester United basu sake nuna sha’awarsu ba ta neman dan wasan sakamakon yanzu sunada cikakkun ‘yan wasan tsakiya wanda hakan yabawa Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid damar neman dan wasan ita kadai.
A satin daya gabata Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta sallami kociyanta Santiago Solari inda kuma ta maye gurbinsa da tsohon kociyanta Zinadine Zidane wanda kuma aka bayyana cewa Kungiyar ta ware masa kudi kusan fam miliyan 300 domin siyan sababbin ‘yan wasa a kakar wasa mai zuwa.
Dan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea, Edin Hazard da dan wasan tsakiya na Tottenham, Christian Eriksen suma suna daga cikin ‘yan wasan da ake ganin sabon kociyan na Real madarid zai nema a kakar wasa mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!